Home Back

Tinubu Ya Bai Wa Minista Wa’adin Kwana 2 Don Samar Da Tsarin Mafi Ƙarancin Albashi

leadership.ng 2024/7/1
Tinubu Ya Nemi Jihohi Su Dakatar Da Karbar Haraji A Kan Masu Safarar Kayan Abinci

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa ministan kudi, Wale Edun wa’adin sa’oi 48 domin gabatar masa da sabon tsarin mafi karancin albashin ma’aikata zai ci domin nazari da kuma daukar mataki a kai.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris ne, ya sanar da umarnin bayan wata ganawar da shugaba Tinubu ya yi da kwamitin da ke tattaunawa da NLC, jim kadan bayan dakatar da yajin aikin da suka fara a ranar Litinin.

Idris, ya bayyana cewar bangarorin biyu, wato na gwamnati da kuma shugabannin kwadago za su ci gaba da ganawa a tsakaninsu domin cimma yarjejeniya a kan sabon tsarin mafi karancin albashin cikin mako guda.

Ministan, ya ce daga cikin umarnin da Tinubu ya bayar, har da bukatar ganin wakilan bangarorin biyu sun amince da kudin da ‘yan Nijeriya za su gamsu da shi, Wanda kuma gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu za su iya biya ba tare da fuskantar matsala ba.

Idan ba a manta ba kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun shiga yajin aiki a ranar Litinin kan neman a kara mafi karancin albashin ma’aikata.

A ranar Talata suka tsagaita da yajin aikin domin ci gaba da tattaunawa da gwamnatin tarayya da nufin nemo mafita.

People are also reading