Home Back

WAƘA DAGA BAKIN MAI ITA: ‘Mun raya matattu fiye da 50 bayan sun mutu murus – Fasto Oyakhilome

premiumtimesng.com 2024/4/30
WAƘA DAGA BAKIN MAI ITA: ‘Mun raya matattu fiye da 50 bayan sun mutu murus – Fasto Oyakhilome

Fasto Chris Oyakhilome ya jangwalo yi masa yamaɗiɗi a soshiyal midiya, bayan ya yi iƙirarin raya matattu 50 da ya yi bayan sun mutu.

Oyakhilome ya yi iƙirarin haka a lokacin da ya ke taron addu’o’in kwanaki uku na warkar da masu fama da lalurori, a cocin sa da ke LoveWorld, Amurka.

Ya yi taron kwanaki ukun daga 15 zuwa 17 ga Maris, 2024.

A cikin wani bidiyon da aka watsa kai-tsaye shafin LoveWorld USA na Facebook, a ranar 17 ga Maris, faston ya ce ya raya matattu 50 da suka haɗa da masu shekaru daban-daban kuma ‘yan ƙasashe daban-daban.

“Cikin shekarar da ta gabata mun raya matattu fiye da 40.

“Wasu har cikin asibiti muka je muka raya su a gaban likitoci. To me za ku ce kan wannan?”

Ya yi shaguɓe ga waɗanda ba su yarda da raya matattun da ya ce ya ke yi, har ya na cewa wai wasu na ganin cin hanci mu ke ba su daga lahira domin su dawo duniya.

Sai dai kuma bai gabatar da ko mutum ɗaya da ya bada labarin abubuwan da ya gano a barzahu kafin a dawo da shi duniya ba.