Home Back

Najeriya ta fara shirin aika mutum ya duniyar wata

premiumtimesng.com 2024/7/6
Najeriya ta fara shirin aika mutum ya duniyar wata

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta na shirye-shirye aika ɗan Najeriya na farko a duniyar wata, domin ya je, ya dawo kuma ya ƙad-da abin da ya gano.

Darakta Janar na Hukumar Binciken Sararin Sama, Mathew Adepoju ne ya bayyana haka, yayin da ya ke wa taron manema labarai bayani a Abuja, a ranar Laraba.

Adepoju ya ce za a tura tura zakaran gwajin dafi bisa wata haɗin gwiwa tsakanin hukumar sa da kuma Cibiyar Binciken Sararin Sama ta SERA.

Wannan haɗin gwiwa a cewar sa, “zai bayar da kuma samar da ƙofar damar faɗaɗa binciken kimiyya da inganta fasahar zamani.”

Najeriya, ƙasar da ta kasa gyara dukkan matatun ɗanyen mai na ƙasar, tsawon shekaru da dama ta dogara da sayo fetur daga ƙasashen waje. Wannan dalili ne kuma ya haifar da masifar tsadar sa, lamarin da ya sa tun farkon wannan gwamnatin aka cire tallafin fetur.

Haka kuma, a matsayin ƙasar na ƙasaitacciya a Afirka, har yau ta kasa farfaɗo da Kamfanin Sufurin Jiragen Sama na Nigeria Airways, ta yadda ƙasar ba ta da jirgi ko ɗaya.

People are also reading