Home Back

An Gurfanar Da Mutane 5 Kan Zargin Fashi Da Makami

leadership.ng 2024/6/1
Kotu Ta Daure Basarake Shekaru 15 Saboda Garkuwa Da Kansa

An gurfanar da mutane biyar a wata kotun majistare da ke yankin Iyaganku a Ibadan, kan zargin aikata fashi da makami. 

Ana tuhumar mutane biyar din da laifin hada baki da fashi da makami.

Mai gabatar da kara, Insifekta Olalekan Adegbite, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne da misalin karfe 2 na daren ranar 8 ga watan Janairu, 2p24 a yankin Olode a Ibadan.

Adegbite, ya bayyana cewa wadanda ake tuhumar sun kai hari yankin da makamai tare da yi wasu mutane fashin wayoyi da wasu kayayyaki.

“Sun je yankin da bindigogi da wasu makamai, sun kai hari tare da yi wa mutane fashin wayoyi da sauran kayayyaki,” in ji shi.

Adegbite, ya ce laifin ya saba da sashe na 6 (b) da na 1 (2) na dokokin fashi da makami na Nijeriya na 2004.

Alkalin kotun, Misis Oluwabusayo Osho ba ta yanke hukunci ba, saboda rashin gamsassun hujojji.

Ta bayar da umarnin mayar da karar zuwa ga daraktan kararrakin jama’a don neman shawara.

Bayan haka Osho ta dage shari’ar har zuwa ranar 29 ga Afrilu, 2024.

People are also reading