Home Back

“Hanyoyi 6 Na Dawo da Martabar Najeriya”: Atiku Ya Soki Manufofin Gwamnatin Tinubu

legit.ng 2024/7/3

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya ce manufofin shugaban kasa Bola Tinubu a shekara daya sun gaza samar da ci gaba a Najeriya.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Atiku Abubakar wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, ya zargi Tinubu da kawo tsare-tsare da suka kara talauta talakawa da gurgunta masu hannu da shuni.

Sai dai ya bayyana matakai guda shida da shugaba Tinubu zai dauka domin samun nasarar dawo da martabar Najeriya, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Atiku ya yi magana kan tattalin arzikin Najeriya
Atiku ya ba gwamnatin Tinubu shawarwari kan tattalin arziki. Hoto: @atiku, @officialABAT Asali: Twitter

Shugaban, wanda ya hau karagar mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, tare da manufar 'samar da sabuwar Najeriya", ya cika shekara daya a kan karagar mulki a yau Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Premium Times ta ruwaito Atiku ya caccaki gwamnatin jam’iyyar APC kan rashin tabuka komai a fannin gyara tattalin arziki a ckin shekara daya.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya ba gwamnatin Tinubu satar amsar yadda za a ceto tattalin arzikin kasar.

1. Samar da tsari na gudanar da ayyuka

Atiku Abubakar ya ce:

"Da farko, akwai bukatar gwamnati ta waiwayi manufofinta. Ya zama wajibi ta yarda cewa ana aiwatar da sauye-sauye ne mataki bayan mataki.
Ana buƙatar tsarin da zai fayyace manufofin yin sauye-sauye da kuma dabarun da aka dauka domin tabbatar da sauyin ya yi amfani."

2. Waiwayar kasafin kudin 2024

Shawara ta biyu da Atiku ya ba gwamnatin Tinubu ita ce:

"Ya zama wajibi gwamnati ta gudanar da cikakken nazari kan kasafin kudin shekarar 2024 a cikin sabon tsarin gudanar da muka ambata a baya.
"Idan har muka kalli kasafin 2024, babu wani abin a zo a gani a ciki. Kasafin ba zai gyara tattalin arziki ko bunkasa rayuwar 'yan kasar ba."

3. Waiwayar shirin ba da tallafi na SIP

Hanya ta uku a cewar tsohon mataimakin shugaban Najeriya ta ce:

"Gudanar da cikakken nazari da garambawul ga shirin ba da tallafin jari ga jama'a (SIP) domin rage wahalhalun da manufofin gwamnati suka haifar a kan talakawan kasar.
"Akwai bukatar shirin SIP ya ba da fifiko wajen tallafawa kananaun 'yan kasuwa ba iya daidaikun mutane kadai ba domin da su ne za a cimma nasarar tattalin arziki."

4. Waiwayar haraji da gwamnati ke sakawa

Atiku Abubakar ya kara da cewa dole ne Tinubu ya yi taka-tsantsan kan duk wani yunkuri na kara talautar da talakawa ta hanyar bullo da sababbin haraji ko kara kudin haraji.

Ya ce:

“Muna sane da yunkurin da ake yi na kara kudin harajin VAT daga kashi 7.5 zuwa kashi 10, da sake dawo da haraji kan harkokin sadarwa, da kuma kara yawan kudaden haraji kan kayayyaki da dama."

5. Waiwayar batun janye tallafin fetur

Shawara ta 5 da jagoran 'yan adawa na Najeriya ya ba Tinubu ita ce:

"Ba da ba'asi game da tsarin tallafin man fetur, gami da yadda janye tallafin ya yi tasiri ga kasafin kuɗi da kuma fa'idar janye tallafin ga kudaden da ake rabawa tarayya da jihohi.
"Adadin gangar mai nawa na fetur ake shigo da shi tare da rarrabawa, kuma a wane farashi? Tallafin nawa ake kashewa wajen aiwatar da hakan? Akwai bukatar gwamnati ta yi bayani."

6. Sake fasalin tsaron Najeriya

Atiku Abubakar dole ne Shugaba Tinubu ya sake fasalin hukumomin tsaron kasar domin abin da ke faruwa yanzu ya nuna baraka karara a harkar samar da tsaro a Najeriya.

Ya ce halin da ake fama da shi na rashin tsaro yana ci gaba da yin illa ga noma da kuma rage kima ga tattalin arzikin kasar, musamman a sassan Arewacin kasar nan.

Har yanzu Tinubu bai nada jakadai ba

A wani labarin mun ruwaito cewa har zuwa wannan rana ta Laraba da Shugaba Bola Tinubu ke cika shekara daya a kan mulki, bai nada jakan Najeriya zuwa kasashen waje ba.

Ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya ce Najeriya na fuskantar babban kalubalen kudi da tabarbarewar tattalin arziki ya sa Tinubu bai nada jakadan ba.

Asali: Legit.ng

People are also reading