Za a zabga ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihohi 9 a Najeriya daga ranar Laraba – Hasashen NiMet
Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) a ranar Talata ta ce akwai yiwuwar samun ruwan sama a wasu jihohin kasar daga ranar Laraba zuwa Juma’a.
Ana sa ran samun ruwan sama kamar da bakin kwarya daga safiyar yau Laraba a sassan Oyo, Kwara, Osun, Ekiti, Ondo, Kogi, Bayelsa, Ribas, Akwa Ibom, Cross River, Benue, Taraba, Plateau, Niger, Ogun, Kaduna, babban birnin tarayya da jihar Zamfara.
NiMet ta kuma yi hasashen cewa za a samu iska mai karfi a lokacin ruwan saman a sassan Oyo, Kwara, Osun, Ekiti, Ondo, Kogi, Bayelsa, Ribas, Akwa Ibom, Cross River, Benue, Taraba, Plateau, Niger, Ogun, Kaduna, Babban Birnin Tarayya. da jihohin Zamfara.