Home Back

‘Renewed Hope’: Ministan Tinubu Ya Raba Buhunan Shinkafa 10,000 a Jihar Oyo

legit.ng 2024/6/26
  • Sama da gidaje 10,000 a jihar Oyo ne suka amfana da tallafin buhunan shinkafa 10,000 daga shugaba Bola Tinubu
  • Wadanda suka amfana sun hada da 'yan kasuwa, kungiyar kwadago, kungiyar 'yan jarida, dalibai, da dai sauransu
  • Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce an ba da tallafin shinkafar ne domin rage radadin da jama'a ke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Oyo - Ministan wutar lantarki, Cif Adebayo Adelabu, ya raba buhunan shinkafa sama da 10,000 ga dalibai, kungiyoyin kwadago, 'yan kasuwa da sauran su a jihar Oyo.

Gwamnatin tarayya ta ba tallafin shinkafa a jihar Oyo
Oyo: Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya ba raba buhuna 10,000 na shinkafa a Oyo. Hoto: @federal_power Asali: Twitter

A cewar ministan, tallafin abincin na daga cikin tsare-tsaren gwamnatin shugaba Bola Tinubu na ‘Renewed Hope,’ jaridar Tribune ta ruwaito.

"Manufar ba da tallafin shinkafar" - Adelabu

Wadanda suka amfana da tallafin sun hada da Mogajis na kasar Ibadan, kungiyar 'yan kasuwa, kungiyar kwadago (NLC), kungiyar 'yan jarida (NUJ), kungiyar TAMPAN, kungiyar ɗalibai da sauran su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a Ibadan a lokacin ba da tallafin, Adelabu ya bayyana cewa shinkafar ta fito ne daga fadar shugaban kasa domin rage radadin da mutane ke ciki.

Jaridar The Nation ta ruwaito ministan yana cewa shugaba Tinubu na sane da irin wahalar da ‘yan Nijeriya ke ciki, inda ya ba da tabbacin cewa wahalar ta wucin gadi ce.

Gidaje 10,000 sun amfana da tallafin Tinubu

Ministan ya ce:

“Shugaba Tinubu ya yanke shawarar ba mu namu kason a jihar Oyo, kuma wannan tallafin ba shi da alaka da siyasa sai dai ma nuna shugabanci nagari.
“Ina so in yi kira ga jama’a da su ci gaba da marawa gwamnatin Tinubu baya, abin da muke bukata daga gare ku shi ne ci gaba da yin addu’o’i kan Allah ya bamu ikon gyara kasar nan."

An ruwaito cewa sama da gidaje 10,000 ne suka amfana da wannan tallafin abincin na gwamnatin tarayya a jihar.

Sauki zai samu, abinci zai wadata - Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito maku cewa Shugaba Bola Tinubu ya ba 'yan Najeriya tabbacin cewa Najeriya za ta fita daga wannan matsin tattalin arzikin da take ciki.

A yayin da ya ke nuni da samuwar sauki nan gaba, Tinubu ya kuma yi alkawarin wadatar da 'yan kasar da abinci ta hanyar inganta harkar noma a fadin jihohi.

Asali: Legit.ng

People are also reading