Home Back

Irin Hikima Da Karfin Da Suka Ba Da Muhimmin Tasiri

leadership.ng 2024/5/19
Irin Hikima Da Karfin Da Suka Ba Da Muhimmin Tasiri

A ranar 26 ga watan Afrilu na shekarar 2024, an yi wani bikin nune-nunen hotuna na musamman a birnin Beijing.

A yayin bikin, mai daukan hotuna daga kasar Faransa Gregoire de Gaulle, ya nuna hotunan da ya dauka cikin shekaru 40 da suka gabata a kasar Sin, wadanda suka nuna ci gaba da sauye-sauyen da aka samu a kasar Sin.
Sabo da tasirin da tsohon yare suka yi masa, Gregoire de Gaulle yana son kasar Sin sosai, kuma dan uwan mahaifinsa shi ne shugaban farko na Jamhuriyar Faransa Ta Biyar wato Charles de Gaulle.

A shekarar 1964, shugaba Charles de Gaulle ya tsaida kudurin kafa huldar diflomasiyya a tsakanin kasarsa da Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin. Wannan kuduri mai ma’ana da ya aiwatar, ya bude sabon babin dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu, haka kuma, ya kasance muhimmin batu cikin harkokin siyasar kasashen duniya, wanda ya kafa tushen hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasar Faransa cikin dogon lokaci.

A ranar 25 ga watan Janairu na shekarar 2024, a yayin bikin taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar huldar diflomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasar Faransa, shugaban kasar Sin ya bayyana cewa, harkar kulla huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu a shekarar 1964, ta kasance babbar harkar siyasa da ta faru cikin tarihin kasashen duniya. Shugaban kasar Sin na lokacin, Malam Mao Zedong, da shugaban kasar Faransa na lokacin, Malam Charles de Gaulle, sun nuna himma da karfinsu, wajen bude kofar hadin gwiwar dake tsakanin yammacin kasashen duniya da gabashin kasashen duniya, lamarin da ya samar da damammaki, da fata ga kasashen dake cikin Yakin Cacar Baki.

Ya zuwa yanzu, shekaru 60 bayan faruwar hakan, an samu sakamako masu kyau bisa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Faransa, wadanda suka nuna nasarar mu’amala a tsakanin gabashin kasashen duniya da yammacin kasashen duniya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

People are also reading