Home Back

Mutane 75,000 Sun Kamu Da HIV, 45,000 Sun Rasu A Shekarar 2023 – NACA DG

leadership.ng 3 days ago
Mutane 75,000 Sun Kamu Da HIV, 45,000 Sun Rasu A Shekarar 2023 – NACA DG

Dr. Temitope Ilori, Darakta-Janar na Hukumar yaƙi da HIV ta ƙasa (NACA), ya bayyana cewa, mutane 75,000 sun kamu da cutar cuta mai karya garkuwar jiki da kuma mutuwar mutane 45,000 masu alaka da cutar kanjamau a shekarar 2023.

Da yake jawabi a wani taron kwana biyu na kwamitin yadda za a shawo kna cutar (National Prevention Technical Working Group (NPTWG) ) taron da aka yi a Abuja, Ilori ya bayyana buƙatar gaggawar aiwatar da shawarwarin da aka bayar daga taron rigakafin cutar a Nijeriya na shekarar 2024 domin cimma burin kawar da cutar HIV nan da shekarar 2030.

Duk da raguwar sabbin cututtukan da aka samu, Ilori ya nuna damuwa game da yawan adadin da yanzu haka suke akwai kuma ya jaddada cewa yawan yaɗa cutar daga Uwar-zuwa-jariri ya kasance ƙasa da yadda suke burin ganin ya ragu.

Farfesa Muhammad Pate, ministan kula da lafiya da walwalar jama’a, ya jaddada mahimmancin karfafa dabarun wayar da kai don hana sake bullar cutar HIV. Pate wanda ya samu wakilcin Dakta Bashorun Adebobola, ya bukaci masu ruwa da tsaki da su sake duban irin ci gaban da aka samu kan dabarun rigakafin cuta mai karya garkuwar jikin.

Dr Leo Zekeng, daraktan hukumar UNAIDS a Nijeriya, ya bayyana cewa, Ne Nijeriya ba ta kama hanyar cimma muradun rigakafin da aka sanya a shekarar 2025. Ya jaddada buƙatar samar da tsarin gudanar da ayyuka don tabbatar da ana kan turba da bitar ci gaban da aka samu duk bayan wata uku.

Evans Emerson, mataimakin mai lura da ƙungiyar ta PEPFAR, ya nanata ƙudurin Amurka na tallafawa Najeriya da kuɗaɗen da sabbin dabarun yaƙi da cutar HIV.

Bugu da ƙari, NACA ta gabatar da rahoton fasaha da kuma sanarwar taron rigakafin cutar HIV na 2024, tare da jaddada buƙatar ci gaba da ƙoƙarin magance cutar yadda ya kamata.

People are also reading