Home Back

Tsohon Shugaban Ƙasa Ya Faɗi Wasu Gwamnoni da Ke Amfani da Ƴan Daba Su Murde Zaɓe

legit.ng 2024/7/7
  • Dokta Goodluck Ebele Jonathan ya zargi wasu gwamnonin jihohi da amfani da ƴan daba wajen maguɗin zaɓe don cimma burinsu na siyasa
  • Tsohon shugaban ƙasar ya ce maimakon gwamnoni su gina waɗannna matasa +a hanyar da gwamnati za ta amfana su, sun zaɓi mayar da su ɓata gari
  • Jonathan ya yaba da yadda Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya ɗauki yaran da suka kammala digiri da daraja ta farko aiki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan, ya yi zargin cewa wasu gwamnoni na amfani da ɓata gari wajen cimma burinsu na siyasa.

Jonathan ya ce gwamnonin sun mayar da hankali wajen shirya ɓata gari don maguɗin zaɓe, maimakon su taimaka masu su zama kwararru a aikin gwamnati.

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Jonathan ya soki gwamnonin da ke amfani da ƴan daba su murde zabe Hoto: Dr. Goodluck Jonathan Asali: Getty Images

Ya bayyana haka ne a Benin ranar Laraba a wurin kaddamar da sakatariyar jihar Edo da Gwamna Godwin Obaseki ya sabunta, Daily Trust ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban kasar ya ce lokacin da shugaban ma’aikatan Edo ya sanar cewa Obaseki ya dauki ɗaliban da suka gama digiri da kwali mafi daraja aiki, ya ji dadi matuka.

"Mutum mai hangen nesa kamar Obaseki ne kaɗai zai iya haka. A taƙaice mun zo wani zamani da idan ka je wasu jihohin za ka ga gwamnoni suna shirya ɓata gari saboda siyasa.

"Suna ƙarafafawa ɓata gari guiwa domin su yi amfani da su wajen murde zaɓe, su sato akwatu, su ɗauki wukake da makamai suna farmakar mutane a wurin zaɓe.

"Amma a nan Edo kana ƙarfafa masu hazaƙa, mutane masj hazaka ba ƴan jam'iyya ɗaya bane, akwai su a kowace jam'iyya."

- In ji Jonathan.

Tun da farko, Gwamna Obaseki ya ce ya gyara sakatariyar ne saboda yana da yaƙinin cewa dole sai tsare-tsaren gwamnati sun tafi daidai za a samu ci gaba a jihar.

Tinubu ya faɗi dalilin zamewa a Abuja

A wani rahoton Bola Ahmed Tinubu ya yi magana a karon farko kan zamewar da ya yi ya faɗi a lokacin hawa motar fareti a birnin tarayya Abuja.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa shi ɗan yarbawa ne kuma ya ɗan taɓa wasan al'adar da ake kira dobale domin murnar ranar dimokuraɗiyya.

Asali: Legit.ng

People are also reading