Home Back

Majalisar Dinkin Duniya Ta Shirya Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

leadership.ng 2024/7/1
Majalisar Dinkin Duniya Ta Shirya Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

Majalisar Dinkin Duniya ta shirya wani muhimmin taro na masu ruwa da tsaki a kan harkar tsaro, laifuffuka da shaye-shayen miyagun kwayoyi a Jihar Zamfara.

Taron, wanda aka fara shi Litinin da ta gabata a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau, ofishin kula da shaye-shayen miyagun kwayoyi da laifuffuka na Majalisar Dinkin Duniya da ke Nijeriya ne ya shirya shi.

Mai magana da yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a Gusau, ya bayyana cewa taron, wani shiri ne fayyacewa da lalubo hanyoyin mayar da martani game da matsalolin harkar tsaro da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Sulaiman Bala ya kara da cewa, wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya karkashin jagorancin, Oliber Stolpe, wanda kuma shi ne wakili a Nijeriya na UNODC, taron zai tattaro masu ruwa da tsaki, inda za su zauna na tsawon kwanaki uku.

Sanarwar ta ce, “A wani muhimmin abu na masu ruwa da tsaki, ofishin kula da shaye-shayen miyagun kwayoyi da laifuffuka na Majalisar Dinkin Duniya (UNODC) ya shirya wani taron kara wa juna sani na kwana uku a kan harkar tsaro yau a Gusau.

“Taron ya samar da masu ruwa da tsaki na cikin gida da wasu baki daga Majalisar Dinkin Duniya, inda za su yi zuzzurfan nazari domin samar da hanyoyin magance duk wani yanayi na tsaro, laifuffuka da shaye-shayen miyagun kwayoyi a Jihar Zamfara.

“Taron ya bayyana ingantattun ayyuka da kuma hanyoyin da za a bi daga ciki da wajen Nijeriya wajen tunkarar wadannan kalubale don samar da wani shiri na hadin gwiwa.”

A jawabinsa na bude taron, Gwamna Lawal ya jaddada cewa, kwakkwarar ta-waga ta masana daga Majalisar Dinkin Duniya sun nuna aniyarsu ta hadin gwiwa wajen magance kalubalen da ke addabar Zamfara da suka hada da ’yan bindiga da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Ya ce, “Kwanan nan na ziyarci Majalisar Dinkin Duniya domin neman shiga tsakani wajen magance wasu matsalolin da muke fuskanta, inda na samu kyakkyawar alaka da Amina J. Mohammed, mataimakiyar Sakatare Janar ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma sauran bangarorin da take jagoranta ciki har da shugaban ofishin kula da miyagun kwayoyi da sauran laifuka.

“Saboda haka, wannan taron kara wa juna sani shaida ne na himmar da Majalisar Dinkin Duniya ke da shi na cika alkawuran da ta dauka don taimaka mana mu wajen kara fahimtar yadda za mu magance kalubalen da mu ke fuskanta. Muna matukar godiya.

“Sama da shekaru goma, Zamfara tana fama da wadannan matsalolin da ke kawo cikas ga tsaro da zaman lafiyar al’ummarmu da kuma kawo cikas ga ci gaban za-mantakewa da tattalin arziki. Don haka gwamnatina ta dauki wannan ziyara da taron bita da muhimmanci, domin sakamakon zai nuna yadda manufofinmu za su kasance wajen dabarun yaki da wadannan kalubale.

“Na yi farin cikin ganin cewa za a tattauna batutuwa da dama yayin taron wadan-nan sun hada da bayyanar da tushen matsalolin rashin tsaro da aikata laifuka a ji-har, kamar garkuwa da mutane, satar shanu, hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, da rikicin kabilanci, rawar da jami’an tsaro daban-daban na jihohi da cibiyoyin gargajiya suke takawa wajen yakar matsalolin, tallafin Majalisar Dinkin Duniya ga karfafa shari’a a aikata laifuka.

“Hanyoyi da yanayin da ke haifar wa al’umma shaye-shayen miyagun kwayoyi a Jihar Zamfara da wanda za a bi wajen rigakafin shan muggan kwayoyi da sauran muhimman batutuwa, duk an shirya su don tattaunawa a wannan taro.

“Ina kira ga mahalarta taron da su yi amfani da wannan damar kuma su ba da himma don cin gajiyar ayyukan. Ya kamata ku saurara, ku koya, kuma ku ba da gudunmawa mai inganci.

“A karshe, ina fatan dukkanin mahalarta taron za su kasance masu amfanar al’umma. Kamar yadda na bayyana, shawarwarin da aka samar a nan za su kasance masu muhimmanci wajen tsara dabarunmu da ayyukanmu don magance matsalolin da muke fuskanta.”

People are also reading