Home Back

Hankula Sun Tashi Yayin da Wani Soja Ya Hallaka Farar Hula a Abuja

legit.ng 2024/10/5

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Ana zargin wani soja da ba a tantance kowane ne ba ya daɓawa wani bakanike wuka har lahira a birnin tarayya Abuja.

Sojan dai ya aikata wannan aika-aikar ne a ƙauyen Kugbo da ke kan hanyar Keffi zuwa birnin tarayya Abuja.

Soja ya hallaka farar hula a Abuja
Soja ya hallaka bakanike a Abuja Hoto: @HQNigerianArmy Asali: Facebook

Rahoton jaridar The Nation ya bayyana cewa sojan ya daɓawa bakaniken wuƙa ne a ranar Alhamis a lokacin da suke gardama, sannan daga bisani ya ranta ana kare.

Wani bakanike a yankin mai suna, Yusuf Mustapha, ya shaidawa jaridar Daily Trust ta wayar tarho cewa lamarin ya haifar da rikici a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa rikicin ya jawo masu masu kanikanci da masu sayar da kayan gyara suka rufe shagunansu.

Yusuf Mustapha ya ce ƴan sanda sun garzaya wurin domin dawo da zaman lafiya.

"Sojan ya zo ne da bakanikensa domin siyan kayan gyaran mota a kasuwar a ranar Alhamis. Ana cikin haka sai gardama ta ɓarke tsakaninsa da wani bakanike a kasuwar. Sojan sai ya ƙwada masa wani abu a kansa."
"Daga nan sai sojan ya zaro wuƙa. Wani bakaniken ya yi ƙoƙarin hana shi yin amfani da ita. Daga nan sai ya shaƙo bakaniken ya ɗaba masa ita har ya mutu. Ganin abin da ya aikata, sai ya ranta ana. kare. Suna can suna nemansa."

- Yusuf Mustapha

Asali: Legit.ng

People are also reading