Home Back

Mun baza jami’an mu a cikin unguwanni dan magance matsalar tsaro yayin sallar dare – Ƙungiyar Bijilanten Kano

dalafmkano.com 2024/5/17

Ƙungiyar sintirin Bijilante ta ƙasa reshen jihar Kano, ƙarƙashin babban kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta ce ta baza jami’an ta 2,500 a lungu da saƙon ƙananan hukumomin Kano 44, domin samar da tsaro a cikin unguwannin Kano, yayin fita sallar dare ta Tuhajjud.

Mai magana da yawun ƙungiyar a matakin jahar Kano, kuma kwamandan ta na ƙaramar hukumar Fagge, Usman Muhammad Ɗan Daji, ne ya bayyana hakan yayin zantwarsa da gidan rediyon Dala FM Kano, a yau Lahadi, ya ce za su zuba jami’an su aƙalla 2500, da za su rinƙa zirga-zirga a cikin unguwanni, domin magance matsalar tsaro.

“Duk wanda muka kama da tayar da hankalin al’umma ko satar kayan mutane ko ƙwace yayin tafiya sallar daren ta Tuhajjud, zamu miƙa shi hannun jami’an tsaro domin ɗaukar matakin da ya dace akan mutum babu sassautawa, “in ji Ɗan Daji”.

Ƙungiyar Bijilanten ta jihar Kano ta kuma buƙaci haɗin kan al’umma, domin ganin an gudanar da sallar cikin kwanciyar hankali ba tare da fuskantar wata matsala ba.

People are also reading