Home Back

"Akwai Wahala": Matar Tsohon Shugaban Kasa Ta Ce Ko Kyauta Ba Za Ta Koma 'Aso Rock' Ba

legit.ng 4 days ago
  • Matar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Patience Jonathan ta magantu kan komawa fadar 'Aso Rock'
  • Patience ta bayyana cewa kwata-kwata ba ta sha'awar komawa fadar shugaban kasa saboda wahalar da ke cikin mulkin Najeriya
  • Tsohuwar 'First Lady' ta ce ko kiranta aka yi ta koma ba ta bukata saboda ta san irin kalubalen da suka fuskanta a lokacin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Matar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ta yi magana kan sake dawowa fadar shugaban kasa.

Patience Jonathan ta ce ba ta sha'awar sake dawowa 'Aso Rock' saboda tsananin wahalar gudanar da mulkin Najeriya.

Patience ta bayyana haka a cikin wani faifan bidiyo da TVC News ta wallafa yayin wani babban taro da ta halarta.

Ta ce ko kiranta aka yi ta koma fadar shugaban kasa ba ta so domin ta san irin wahalar da ke ciki.

"Idan ka kira ni na koma 'Aso Rock' ba zan je ba, saboda tsananin dzz wahalar da ke ciki, ba kaga yadda na ke ba yanzu."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mulkin Najeriya akwai wahala, idan Ubangiji ya fito da kai daga fadar shugaban kasa ka gode masa saboda ya maka gata."
"Ya fito da kai daga can, mene dalilin sai ka koma, ba zan taba komawa ba nikam."

- Patience Jonathan

Taohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya karbi mulkin Najeriya ne a shekarar 2010 bayan rasuwar marigayi Umaru Musa Yar'adua.

Jonathan ya tsaya takara a zaben shugaban kasa a shekarar 2011 inda ya yi nasara kan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Har ila yau, a zaben 2015 sun sake karawa inda Buhari ya yi nasarar kwace mulkin PDP da ta shafe shekaru 16 a lokacin tana mulkin Najeriya.

Jonathan ya bukaci karin haƙuri a Najeriya

Kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya ce nan ba da daɗewa ba Najeriya za ta shawo kan ƙalubalen tattalin arziƙin da ke addabarta.

Goodluck Jonathan ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya na yin iyakacin ƙoƙarinta wajen ganin ta shawo kan matsalar.

Asali: Legit.ng

People are also reading