Home Back

Gwamna Dauda Lawal Ya Kinkimo Wani Muhimmin Aiki a Zamfara

legit.ng 2024/7/2
  • Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta ƙaddamar da aikin gyaran asibitin ƙwararru na Ahmad Sani Yariman Bakura
  • Aikin gyaran asibitin za a yi shi ne domin ƙara bunƙasa ayyukan samar da kiwon lafiya ga al'ummar jihar
  • Gwamna Dauda ya bayyana cewa za a ɗaga darajar asibitin zuwa matsayin asibitin koyarwa na jami'ar jihar Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da aikin gyaran asibitin ƙwararru na Ahmad Sani Yariman Bakura da ke Gusau.

Wannan matakin gyaran asibitin mallakin jihar Zamfara na da nufin mayar da shi zuwa asibitin koyarwa na jami'ar jihar.

Dauda Lawal ya fara gyaran asibiti a Zamfara
Gwamna Dauda Lawal ya kaddamar da aikin gyaran asibitin kwararru na Zamfara Hoto: Dauda Lawal Asali: Facebook

Gwamna Dauda ya ƙaddamar da aikin gyara

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata samarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Juma'a a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da aikin, Gwamna Dauda ya jaddada muhimmancin aikin wajen magance ƙalubalen kiwon lafiya a jihar.

"A yau mun zo ne domin fara gyara da ingantawa da kuma sanya kayan aiki na asibitin kwararru na Ahmad Sani Yariman Bakura Gusau."
"Hakan ya zama wajibi duba irin tarin ƙalubalen da muka gaɗa a ɓangaren lafiya a lokacin da muka karɓi ragamar mulki."

- Dauda Lawal

Gwamnan ya bayyana halin da asibitin ke ciki a halin yanzu, inda ya bayyana shi da cewa yana cikin mawuyacin hali duk da muhimmiyar rawar da yake takawa wajen samar da ayyukan kiwon lafiya.

Za a ɗaga darajar asibitin

Har ila yau, wani ɓangare na inganta asibitin shi ne shirin ɗaga darajarsa zuwa matsayin asibitin koyarwa na jami'a.

Gwamnan ya ƙara da cewa:

"Muna da niyyar mayar da asibitin Yariman Bakura asibitin koyarwa na jami’ar jihar Zamfara da zarar kwalejin kimiyyar lafiya ta fara karatunta."

Gwamna Dauda ya fara biyan sabon albashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta fara biyan mafi karancin albashi na N30,000 ga ma’aikata a jihar da ke yankin Arewa maso Yamma.

Hakan ya biyo bayan alƙawarin da Gwamna Dauda Lawal ya ɗauka yayin ganawa da shugabannin ƴan kwadago a makonnin da suka gabata.

Asali: Legit.ng

People are also reading