Home Back

Tinubu, Ka Taka Wa Wike Birki Ko Ka Fadi Warwas A Abuja A 2027 – Shugabannin APC

leadership.ng 2024/5/4
Babu Wani Shiri Na Kwaso ‘Yan Nijeriya Daga Falasdin Ko Isra’ila –Gwamnatin Tarayya

Shugabannin APC a Abuja sun bayyana wa Shugaban kasa, Bola Tinubu cewa idan har bai taka wa ministan Abuja, Nyesom Wike birki ba, zai fadi warwas a zaben shugaban kasa na 2027, domin ko kuri’a da kashi 2 bisa 100 ba zai taba samu ba a yankin sakamakon yadda Wiken yake kashe jam’iyyar a Abuja. 

Haka kuma sun bayyana cewa lallai jam’iyyar za ta iya rasa zaben kananan hukumomi matukar aka kasa daukan mataki. Sun dai yi ikirarin cewa ministan na kashe siyasar jam’iyyar APC a Abuja sakamakon rashin ganin darajar jam’iyyar da shugabanninta.

Shugabannin jam’iyyar sun bayyana hakan ne a wani taron ‘yan jarida a Abuja, inda mambobin jam’iyyar suka koka kan nade-naden da Wike ya yi a ‘yan kwanakin nan.

Jiga-jigan shugabannin jam’iyyar karkashin jagorancin, Kwamared Abdulwahab Ekekhide da Dabid Omobolaji Obaje, sun ce tun lokacin da ministan ya kama aiki har zuwa yau bai taba zantawa da shugabannin jam’iyyar ba, duk da cewa jam’iyyar ta rubuta masa wasika na neman zantawa da shi, amma ya ki bayar da daman ganinsa.

Idan za a iya tunawa dai, Wike dan jam’iyyar PDP ne, amma Shugaba Tinubu ya nada shi ministan Abuja.

Ekekhide ya ce shugabannin da dukkan ‘ya’yan jam’iyyar APC a Abuja sun yi watsi da mukaman da ministan yake bayarwa, kuma suna ganin ministan yana hakan ne a matsayin cin mutuncin jam’iyyar APC a Abuja.

Ya ce, “Muna kira ga shugaban kasa wanda shi ne ya nada minista da ya ja masa kunne, saboda kauce wa rashin samun ko da kashi biyu na kuri’un da za a kada a zaben shugaba a 2027 da kuma zaben kananan hukumomi idan har ya kasa daukai kararen matakai.

“Kamar yadda muka sani, shugaban kasa yana sama da minista domin shi ne ya nada shi, kuma ya kasance wakilinsa, amma Wike yana cin dunduniyar shugaban kasa a kujeran ministan Abuja.

“Watannin baya da suka gabata, Wike ya  bayyana cewa babu wanda ya isa ya kashe masa siyasa a Jihar Ribas, amma kuma yanzu shi yana kashe siyasar shugaban kasa a Abuja.

“Dalilan da ya sa APC ta yake rashin nasara a Abuja a kowani zabe shi ne, ana nada ministoci wadanda ba su da wata akala siyasa a yankin gundumar Abuja, idan zabe ya zo sukan koma yankunan da suka fito su bar ganin Abuja, idan har ba a karfafa shugabanni da mambobin jam’iyyar ba ta yaya za a samu nasarar lashe zabe,” in ji shi.

People are also reading