Yajin Aiki: ’Yan Ƙwadago Sun Fatattaki Jama’a Daga Cikin Wani Bankin Legas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Legas - An kwashi 'yan kallo a wani bankin Polaris da ke jihar Legas a ranar Litinin bayan da mambobin kungiyar kwadago na NLC suka dura bankin.
'Yan kwadagon sun dura bankin tare da fatattakar abokan hulda domin tabbatar da bin umarnin kungiyar na shiga yajin aikin gama gari.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan kwadagon ba su bar bankin ba sai da suka tabbatar sun fatattaki kowa tare da rufe bankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan kwadago sun rufe sakatariyar jihar Legas da ke Alausa domin tabbatar da yajin aikin da suka shiga.
A yayin da su ke rangadi a fadin jihar ne 'yan kwadagon bisa jagorancin Kwamred Funmi Sessi suka kutsa bankin na Polaris da ke Alausa.
Jaridar Vanguard ta ruwaito kungiyar kwadago ta NLC reshen jihar Imo ta rufe bankuna, sakatariyar jiha da ta tarayya bisa bin umarnin uwar kungiya na shiga yajin aiki.
Sakataren yada labarai na NLC na jihar, Ifeanyi Nwanguma, shine ya bayyana hakan ga manema labarai yayin yajin aikin.
A wani labarin, mun ruwaito kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya (PASAN), ta rufe kofar shiga ginin da wasu motocin bas guda biyu.
PASAN wadda ke bin umarnin kungiyar NLC ta kuma katse wuta da ruwan ginin majalisun biyu, domin tabbatar da an bi umarnin shiga yajin aiki a fadin kasar.
Yajin aikin kungiyoyin kwadago na Najeriya NLC da TUC na ci gaba da daukar zafi a babban birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng