Sojojin Najeriya sun Fatattaki 'Yan Ta'adda, an Kamo Miyagu a Abuja da Oyo
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Rundunar sojojin Najeriya ta samu galaba kan wasu masu garkuwa da mutane dake cin kasuwarsu a Abuja da jihar Oyo.
A wani samame da jami'an sojojin suka kai maboyar 'yan ta'addan a Ajegunle Mpape dake Abuja, sun koro bata-garin tare da cafke mutane uku.
A jawabin da rundunar ta wallafa a shafinta na X, an kai samamen ne bayan samun bayanan sirri na ayyukan 'yan ta'adda yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar sojojin kasar nan ta kama wasu mutane uku a karamar hukumar Bwari dake Abuja bisa zargin tattaro bayanai, suna mikawa masu garkuwa da mutane.
Leadership News ta tattaro cewa an kama Ashiru Muhammed da wasu mata guda biyu; Raham A bubakar da Sadiya Mohammed a samamen.
Sojojin sun samu nasarar gano bindiga kirar Pistol da alburusai 21 da katin cirar kudi (ATM) na bankuna biyar daga maboyar bata-garin.
Sauran abubuwan da aka kwace sun hada da miyagun kwayoyi da wayoyin hannu guda biyu, kuma an tattare su duka zuwa rundunar.
Wani Usman Mohammed Aliyu ya shiga komar sojoji a yankin Igboho-Igbeti dake jihar Oyo lokacin da ake bincike a kan hanyar bayan samun rahoton sirri kan zirga-zirgar bata-gari a yankin.
An kama shi da kudi ₦400,000, kuma ya amsa satar shanu da mutane a yankunan. Rundunar sojojin ta ce ana zurfafa bincike kafin daukar matakin da dace.
A baya mun kawo muku labarin cewa hedikwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta kalubalanci Gwamnatin jihar Katsina kan zargin wasu daga jami'anta na hada baki da 'yan ta'adda.
DHQ ta mayarwa gwamna Dikko Radda raddi, inda ta ce dukkanin jami'anta na biyayya ga kundin tsarin mulkin kasa, kuma ta 'yan Najeriya ce.
Asali: Legit.ng