Home Back

Bukukuwan Sallah: Rundunar ‘Yansanda Ta Kama Bata-gari 104 Da Ake Zargi Da Aikata Laifuka A Kano

leadership.ng 2024/5/13
Fataucin Yara

Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta ce ta kama wasu bata-gari 104 da ake zargi da aikata laifuka a wurare daban-daban a fadin jihar yayin gudanar da bukukuwan Sallah da aka kammala.

Kwamishinan ‘yansandan jihar, Usaini Gumel, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya cewa, an kama wadanda ake zargin da muggan makamai masu launi daban-daban a lokacin bukukuwan.

Gumei ya ce, rundunar ta himmatu wajen tunkarar duk wasu bata-gari da masu daukar nauyinsu da ke kokarin kawo cikas a zaman lafiyan da ake samu a jihar.

Ya bayyana cewa, an samar da isassun matakan tsaro don tabbatar da zaman lafiya a ciki da wajen birnin.

People are also reading