Jihar Kogi Ta Kulla Yarjejeniyar Bunkasa Noma Da Kungiyar Solidaridad
Gwamnatin Jihar Kogi ta kulla yarjeniya da kungiyar aikin noma ta kasa da kasa (Solidaridad), don kara bunkasa fannin aikin noma da kuma kara samar da wadataccen abinci a jihar da ma kasa baki-daya.
Gwamnan Jihar, Ahmed Usman Ododo ne ya bayyana haka a lokacin kaddamar da aikin noma kashi na biyu da aka gudanar a babban birnin tarrayya Abuja.
Ododo ya bayyana hakan ne ta bakin Sakatariyar Gwamnatin Jihar, Dakta Folashade Arike Ayoade.
Har ila yau, ya bayyana cewa; gwamnatin tasa ta sha alwashin inganta
aikin noma a jihar, musamman duba da ganin yadda ta mallaki babbar gonar da ke garin Suleja a jihar.
A cewar tata, Allah ya albarkaci jihar da dimbin damammaki a wannan bangare na aikin noma tare kuma da ingantacciyar kasar noman.
Har ila yau kuma, ta yaba wa kungiyar ta Solidaridad da kuma NIPCONS, bisa tunawa da jihar ta Kogi a bangaren aikin noma da suka yi.
Folashade ta kuma bayar da tabbacin mayar da hankalin gwamnatin jihar, wajen kara habaka fannin aikin noma a fadin jihar baki-daya.
Haka zalika, ta yaba wa Gwamnatocin Kasar Amurka da Netherlands; kan yin hadaka a kan shirin na habaka aikin noma na jihar.
Ta kara da cewa, babu shakka al’ummar jihar da dama sun amfana da ayyukan wannan kungiya ta NISCOPS.
Ta ci gaba da cewa, bisa kaddamar da kashi na biyu na kungiyar NISCOPS a jihar, sannan Gwamnatin Jihar Kogi a shiye take wajen yin hadaka da kunyoyin Solidaridad da kuma IDH, domin amfana da karin wasu shiye-shiryensu, musamman don samar da sakamako mai matukar kyau.
“Bisa rattaba hannun yarjejeniyar da kananan hukumomi uku suka yi da wannan kungiya ta Solidaridad, kan shirin masu ruwa da tsaki na noman Kwakwar Manja na kasa (NISCOPS), hakan zai bai wa Jihar Kogi damar mayar da hankali, musamman a kan wannan fanni na noma; don samun gwaggwabar riba.
Folashade ta ci gaba da cewa, “Gwamnatin Kogi ta gode wa Gwamnatocin Kasashen Netherlands da kuma Ingila, kan dabbaka wannan shiri, musamman domin yaki da kalubalen sauyin yanayi, wanda hakan zai kara taimakawa wajen kara samar da wadataccen abinci; ba a jihar kadai ba, har da ma fadin kasa baki-daya.
Shi kuwa shugaban hukumar, Daan Wensing ya sanar da cewa; ana samun karin bukatar Manja, musamman saboda amfanin da yake da shi da kuma neman sa da ake yi a daukacin fadin duniya baki-daya.
Har wa yau kuma ya bayyana cewa, a karkashin shirin hadakar na NISCOPS da Solidariadad, kananan manoma ake bukata su amfana da shirin, ba wadanda suka ci suka tayar da kai ba.