Home Back

Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙara Mafi Ƙarancin Albashi

leadership.ng 2024/6/29
Yajin Aiki: Gwamnatin Tarayya Za Ta Ƙara Mafi Ƙarancin Albashi 

Gwamnatin Tarayya, ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kungiyoyin kwadagon NLC da TUC a wani taron gaggawa da ta gudanar a ranar Litinin.

Taron karkashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya, George Akume a wani yunkuri na kawo karshen yajin aikin da suka fara.

Bangarorin biyu sun shafe sa’oi biyar zuwa shidda suna tattaunawa da juna kuma a karshe sun cimma matsaya a kan wasu batutuwa.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya shaida cewa gwamnati ta amince ta yi kari a kan Naira 60,000 wanda shi ne sabon albashin mafi karanci na ma’aikata da kungiyoyin suka yi watsi da shi.

Ministan ya yi ikirarin cewa a karkashin yarjejeniyar da suka cimma kungiyoyin kwadagon sun amince su janye yakin aiki:

‘’Da farko za su janye yajin aikin nasu, na biyu kuma gwamnati ta yi alkawarin za ta sake duba mafi karancin albashi da ake biyan ma’aikata, Naira 60,000 domin ayi mu su kari’.

”Na uku za a ci gaba da tattaunawa tsakaninmu da ‘yan kwadago, kwamiti da gwamnati ta kafa zai ci gaba da tattaunawa da su na kusan sati daya, kusan kullum za su yi ta ganawa domin a samu sabon tsari na mafi karancin albashin da za a rika biyan ma’aikata” in ji shi.

A dayan bangaren kungiyoyin kwadagon NLC da TUC sun ce za su gudanar taron majalisar koli a ranar Talata da safe domin su tattauna kan matsayar da suka cimma da jami’an gwamnati.

Mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Kwamarade Kabiru Ado Minjibir ya shaidawa cewa an bai wa kwamitin da aka dorawa alhakin tsara sabon albashi mafi karanci kwanaki bakwai ya kamala tattaunawa da su.

People are also reading