Home Back

"Babu Wanda Ya San El Rufai": Shehu Sani Kan Gwagwarmayar"June 12", Ya Yabi Uba Sani

legit.ng 2024/7/5
  • Shehu Sani ya barranta tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da shiga gwagwarmayar "June 12" a Najeriya
  • Shehu Sani ya bayyana haka yayin da ya ke karin haske kan juya maganarsa da aka yi a taron liyafa a birnin Tarayya Abuja
  • Sanatan ya ce lokacin da suke gwagwarmaya babu wanda ya san Nasir El-Rufai amma Uba Sani ya taimake su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya magantu kan rawar Nasir El-Rufai a gwagwarmayar"June 12".

Shehu Sani ya ce babu wanda ya san El-Rufai a lokacin da ake cikin gwagwarmayar dawo da dimukradiyya.

Shehu Sani ya yabawa Uba Sani yayin da ya bude El-Rufai
Shehu Sani ya yi karin haske kan juya maganarsa game da Nasir El-Rufai a gwagwarmayar "June 12". Hoto: Nasir El-Rufai, Shehu Sani, Senator Uba Sani. Asali: Facebook

June 12: Shehu Sani ya bude El-Rufai

Sanatan ya bayyana haka ne a shafin X yayin da yake karin haske kan rashin fahimtar maganarsa da aka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin kalamansa yayin liyafar cin abinci a ranar dimukradiyya, Sanatan ya yabawa Gwamna Uba Sani kan kokarinsa a gwagwarmayar.

Sai dai wasu sun juya masa magana inda suka alakanta maganar da Nasiru El-Rufai madadin Uba Sani.

Shehu Sani ya magantu kan June 12

"Ina son gyara kuskuren da wasu fgidajen jaridu suka yi kan wadanda suka tsaya mana a gwagwarmayar "June 12" ina magana ne kan gwamnan Kaduna, Uba Sani ba tsohon gwamna ba."
"Uba Sani ya kasance da mu da iyalanmu tsawon wannan lokaci a gwagwarmayar da muka yi har zuwa Arewacin Najeriya."
"Ya kasance tare da mu har lokacin da DSS suka kama shi, sannan ƴan sanda suka cafke shi tare da yi masa duka."
"Falana da Mike Ozekhome da Femi Aborishade da sauransu za su shaida haka, amma ba a san El-Rufai ba lokacin gwagwarmayar."

- Shehu Sani

Shehu Sani ya fadawa Tinubu gaskiya

Kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa taken Najeriya ko kundin tsarin mulki ba zai taba hada kan ƴan ƙasar ba.

Sanatan ya bayyana haka ga Bola Tinubu inda ya ce adalci da daidaito shi ne kadai hanyar hadin kan ƴan Najeriya cikin sauki.

Asali: Legit.ng

People are also reading