Home Back

Man City na neman Ait-Nouri, Man Utd na son Gyokeres

bbc.com 2024/5/19
Rayan Ait-Nouri

Asalin hoton, Reuters

Manchester City ta fara tattaunawa da Wolves a kan yuwuwar sayen dan bayan Algeria Rayan Ait-Nouri, mai shekara 22. (Football Transfers)

Tottenham ta taya dan bayan Fulham Tosin Adarabioyo a kokarin da take yi na riga Manchester United saye dan wasan dan Ingila mai shekara. (Teamtalk)

Newcastle na duba yuwuwar daukan Adarabioyo tare da Lloyd Kelly dan bayan Bournemouth kasancewar kwantiragin 'yan wasan biyu 'yan Ingila zai kare a bazara. (Telegraph)

Manchester United na nuna sha'awarta a kan sayen mai kai hari na Sporting Lisbon Viktor Gyokeres amma kuma tana fargabar Liverpool ka iya yi mata nakasu wajen sayen dan Sweden din mai shekara 25. (HITC)

Liverpool za ta iya sayen dan bayan Sporting Lisbon Goncalo Inacio, dan Portugal mai shekara 22, a kan fam miliyan 40. (Football Insider)

Liverpool ta gano mai tsaron ragar tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21 kuma golan Sunderland Anthony Patterson, mai shekara 23 a matsayin wanda za ta iya dauka domin maye gurbin golanta Caoimhin Kelleher, na Jamhuriyar Ireland. (Mail)

Newcastle United ta kara dagewa a kan zawarcin dan wasan RB Leipzig, Benjamin Sesko, don ganin ta doke Manchester United da Chelsea a kan matashin dan wasan mai kai hari na Slovenia. (Teamtalk)

West Ham ta yi tuntuba a kan dan wasan Panathinaikos Fotis Ioannidis, dan Girka. (Football Insider)

Haka kuma West Ham din ta nemi Juan Miranda, na Real Betis amma kuma Brentford, da Crystal Palace da kuma Wolves su ma sona son dan bayan dan Sifaniya. (HITC)

Chelsea za ta kara tsawon kwantiragin dan wasanta na tsakiya na Argentina Enzo Fernandez da na Ukraine Mykhailo Mudryk, daman kuma an kara wa dukkanin 'yan wasan biyu shekara daya a kan dogon kwantiragin da suke da shi. (Sun)

An sanar da AC Milan a kan halin da ake ciki game da dan wasan tsakiya na Fiorentina Sofyan Amrabat, na Moroko, wanda yanzu yake zaman aro a Manchester United. (Rudy Galetti)

Dan bayan Tottenham Djed Spence, dan Ingila wanda a yanzu yake zaman aro a Genoa, na daya daga cikin manyan 'yan wasan da ake sa ran za su bar kungiyar ta London a bazaran nan. (Football Insider)

Manchester City na daya daga cikin kungiyoyin Turai da ke sa ido a kan matashin dan wasan gaba na Porto Cardoso Varela mai shekara 15. (Foot Mercato)

Tsohon kociyan Chelsea da Everton Frank Lampard ya tsame kansa daga masu neman aikin horad da tawagar Kanada. (Telegraph)

People are also reading