Home Back

Ana Fargabar Mutane Sun Mutu Yayin da Ginin Katafaren Otal Ya Rufta a Abuja

legit.ng 3 days ago
  • Mutane sun shiga fargaba a babban birnin tarayya Abuja a lokacin da wani ginin bene mai hawa huɗu ya ruguje ranar Litinin
  • Rahotanni sun nuna cewa ginin wanda ke da alaƙa da Otal ɗin Westbrook ya rufta kuma da yiwuwar ya danne mutane da dama
  • Tuni dai faifan bidiyon ruftawar benen ya bazu a kafafen sada zumunta yayin da jami'ai ke ci gaba da ƙoƙarin ceto a wurin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - An shiga damuwa da fargaba a lokacin da wani ginin bene na Westbrook Hotel ya rushe a yankin Garki da ke birnin tarayya Abuja.

Yanzu haka da muke haɗa wannan rahoton, ana fargabar ginin ya danne mutane da dama yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

Ginin otal a Abuja.
Wani ginin Otal mai hawa huɗu ya ruguje a babban birnin tarayya Abuja Hoto: @Mobilepunch Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, an ce katafaren otal ɗin Westbrook na wani tsohon gwamnan ɗaya daga cikin jihohin Kudu maso Gabas ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abuja: Ana fargabar mutane sun mutu

Wani ganau, wanda ya zanta da jaridar Punch bisa sharadin sakaya bayanansa ya ce akwai yiwuwar wasu sun mutu sakamakon rugujewar ginin ranar Litinin.

Ya ce a kan idonsa aka ciro wasu mutum biyu daga ɓaraguzan ginin kuma tuni aka wuce da su zuwa asibiti.

"Akwai yiwuwar mutanen da ginin ya rufta kansu sun mutu, na ga an ciro mutum biyu kuma an wuce da su zuwa asibiti yayin da ake ci gaba da lalube a wurin.
"Har yanzun jami'an bada agajin gaggawa ba su zo ba ballantana aikin lalubo mutane ya kankama a ɓaraguzan ginin."

Martanin ƴan Najeriya kan ruftawar ginin

Ƴan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu game da ruftawar ginin a soshiyal midiya. Legit Hausa ta tattaro muku wasu daga ciki.

@Simply_Tessy ya ce:

"Da yiwuwar wata ƴar sharholiya ta jawo mijin wata zuwa cikin ginin nan da ya rufta.

@Prinechoke ya ce:

"Kalli ɓaraguzan ginin da hukumomi suka amince da shi kuma aka sa masa ido."

@CryptoSheffy102 ya ce:

"Idan kuka duba ɓaraguzan ginin cikin natsuwa zaku gane an yi amfanu da kayan aiki mara inganci."

Gobara ta tashi a kasuwar Ƙaru

A wani rahoton kun ji cewa a yammacin ranar Alhamis, 27 ga watan Yunin 2024 ne gobara ta tashi a babbar kasuwar Karu da ke babban birnin tarayya Abuja.

An ruwaito cewa gobarar ta kama gadan-gadan yayin da jami'an hukumar kwana-kwana ke iya bakin kokarinsu domin shawo kanta.

Asali: Legit.ng

People are also reading