Home Back

Aisha Humaira Ta Mayar Da Martani Kan Sace Mahaifiyar Rarara

leadership.ng 2024/10/5
aisha humaira

Jaruma a masana’antar Kannywood, kuma ta kusa da mawaki Dauda Kahutu Rarara, Aisha Humaira ta mayar da martani kan wadanda suke yi wa mahaifiyar mawakin da barayi suka sace a gidanta da ke garin Kahutu na Jihar Katsina muguwar fata, dangane wannan jarabawa da ta same ta.

Humaira a wani faifan bidiyo da ta dora a shafinta na Tik Tok ta fara da godiya da fatan alheri ga wadanda suka nuna damuwarsu kuma suka jajanta wa Rarara kan wannan iftila’in da ya samu mahaifiyarsa.
Daga nan sai ta ce tana matukar mamaki da kaico kan wasu mutane da suke yi wa mahaifiyar mawakin muguwar fata don kawai Rarara ya yi wani abin da ya bata masu rayuwa.

Ta tabbatar da cewar duk wanda ya san halayyar mahaifiyar mawakin ba zai yi mata wani fata mai muni ba, saboda bai war Allah ce da ta rike addinin Musulunci hannu bibiyu kuma take salatin ga Annabi a mafi yawan lokuta.

Aisha ta kara da cewar mahaifiyar mawakin a ko da yaushe tana yi masa nasiha kan ya ciyar da mutane daga cikin abin da Allah ya hore masa na dukiy,a domin kuwa duk abin da ka bai wa wani a nan duniya Allah zai biya ka a ranar gobe kiyama.

A cewarta, takan dinga yi masa nasiha tana cewa ina za ka kai kudin da Allah ya hore maka idan har ba ka taimaki al’ummar Annabi ba, kasani Allah ya ba ka wannan dukiya ne domin wasu su samu ta hanyarka ba don ka dinga ci kai kadai ba.

Dangane da zamanta a kauyen Kahutu kuwa, Aisha ta tabbatar da cewa babu yanda Rarara bai yi da mahaifiyar tasa ba kan ta koma Kano da zama, amma ta ki yarda, inda ta nuna ta fi jin dadin zama a cikin ‘yan’uwa da abokan arziki da aka taso tare tun ana yara.

Humaira ta bukaci mutane da su dinga yi wa iyayen wasu fatan alheri domin kuwa duk abin da ka yi wa iyayen wasu shi za a yi wa naka iyayen, kuma babu wanda ya isa ya gujewa kaddara, duk abin da Allah ya nufa kan mutum dole sai ya faru komai dabarar wannan mutumin.

People are also reading