Home Back

Cin Zarafin Daliba: Mahukunta Sun Garkame Makarantar Lead British Ta Abuja

legit.ng 2024/5/17
  • Biyo bayan bidiyon cin zarafin daliba da ya yadu a soshiyal midiya wanda ya tayar da hankalin jama'a, an rufe makarantar Lead British
  • Mahukuntan makarantar sun ba da sanarwar dakatar da karatu na kwanaki uku domin ba su damar yin bincike mai zurfi kan lamarin
  • A ciki bidiyon da wani @mooyeeeeeee ya wallafa a shafin X, an ga yadda wata daliba ke shararawa wata daliba mari ba kakkautawa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar makarantar Lead British da ke Abuja, ta garkame makarantar biyo bayan bidiyon cin zarafin wata daliba ya karade shafukan sada zumunta.

An rufe makarantar Lead British ta Abuja
Abuja: An rufe makarantar Lead British biyo bayan rahoton cin zarafin daliba. Hoto: @mooyeeeeeee Asali: Twitter

Wata mai amfani da shafin X @mooyeeeeeee ce ta wallafa bidiyon yadda wata daliba ke cin zarafin wata dalibar mai suna Maryam Hassan ta hanyar sharara mata mari.

Dalilin rufe makarantar Lead British

Bidiyon ya haifar da tsokacin dubban masu amfani da soshiyal midiya wadanda suka yi kira ga hukumomin makarantar da su binciki lamarin, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani taro da suka yi a ranar Talata, mahukuntan makarantar sun ba da sanarwar dakatar da karatu na kwanaki uku don ba su damar yin bincike mai zurfi kan lamarin.

Wani babba a mahukuntan ya ce matakin rufe makarantar na wani dan lokaci yana da amfani ga dukkanin bangarorin da abin ya shafa.

Makarantar Lead British ta magantu

Jaridar Vanguard ta ruwaito Abraham Ogunkambi, shugaban makarantar Lead British Abuja, ya fitar da wata sanarwa a ranar Talata, dangane da lamarin.

Ya bayyana rashin jin dadi da kuma Allah wadai da makarantar ta yi kan abin da ya faru da dalibar tare da bada tabbaci kan gudanar da sahihin bincike kan lamarin.

Ya kara da cewa tuni makarantar ta tuntubi dalibar da da kuma iyayenta, inda suka dauki matakin tattaunawa da yarinyar domin ganin ba ta fada mummunan yanayi ba.

Bidiyo: Matar aure na neman haihuwa

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito yadda wata matar aure ta dauki bidiyon kanta rike da kayan jarirai tana sharbar kuka tare da yin addu'ar Allah ya bata haihuwa.

An ruwaito cewa matar na fuskantar hantara da mulakanci daga mutane sakamakon jinkirin da ta samu na samun haihuwa. 'Yan Najeriya sun yi martani kan bidiyon.

Asali: Legit.ng

People are also reading