Home Back

Me tattaunawar Putin na Rasha da shugaban Nijar ke nufi?

bbc.com 2024/4/28
..

A ranar Talata ne shugaban mulkin soji a Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya tattauna ta waya da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, inda suka taɓo batun ƙarfafa harkokin tsaro.

Matakin na nuna ƙaruwar dangantaka tsakanin Nijar da Rasha.

Tun a watan Janairu ne ƙasashen biyu suka amince su ƙara inganta ƙawancen tsaro a tsakaninsu lokacin da Firaiministan Nijar Ali Lamine Zeine ya jagoranci wata tawaga zuwa Moscow babban birnin Rasha.

Nijar, ɗaya daga cikin ƙasashe matalauta a duniya, babbar ƙawar ƙasashen Yamma ce a yaƙi da ta'addanci a yankin Sahel, sai dai ta rungumi Rasha a matsayin babbar ƙawar tsaronta tunda aka hamɓarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Mohamed Bazoum a bara.

Shugabannin biyu sun tattauna kan buƙatar inganta ƙawancen tsaro.

Gwamnatin soji a Nijar ta soke ƙawancenta da Amurka ranar 16 ga watan Maris - yarjejeniyar da ta bai wa sojojin Amurka 1,000 damar gudanar da harkokin tsaro a ƙasar.

BBC ta tuntuɓi masana domin jin yadda suke kallon tattaunawar shugabannin biyu da kuma irin tasirin da matakin zai yi ga alaƙar ƙasashen biyu.

'Akwai gyara a matakin sojin Nijar'

Wani masanin diflomasiyya a Jamhuriyar Nijar, Mustapha Abdullahi, ya ce a ganinsa har yanzu akwai gyara a matakin sojojin Nijar da ke mulki wajen yin baya-baya da ƙasashen Yamma kasancewar yarjejeniyar soji kawai aka yanke.

Ya ce a ganinsa har yanzu Nijar ba ta yanke diflomasiyya da Amurka ba "amma fannin guda ne - matsalar tsaro, shi ma yana yiwuwa sanarwar da Nijar ta bayar wataƙila duka biyu ɗin za a samu a shawo kan matsalar domin kowa ya amfana".

"Wannan gwmanatin riƙon ƙwarya ta soji tana mu'amala da ƙasashen Yamma, ko a baya waccan gwamnati da aka hamɓarar ita ma tana yi, amma za a ga yadda za ta kasance." in ji shi.

Ra'ayin ƴan Nijar game da matakin...

Mallam Ibrahim Na Maiwa na ƙungiyar NPCR ya ce abin murna ne ganin yadda hulɗa ta kai ga wannan mataki tsakanin shugabannin biyu.

"Muna cikin lokaci da ya bai wa duka ƙasashe da al'umomi dama ta su yi hulɗa da wanda suke so, muna cikin yanayi na ƴancin kai, muna cikin lokaci da kowa zai zaɓa wa kansa wanda yake so su yi abota da shi."

Sai dai ra'ayin wasu ya banbanta, inda Malam Sule Oumarou shugaban ƙungiyar FCR ya ce yana fatan kwalliya ta biya kuɗin sabulu, "kar ya zama ba girin-girin ba ta yi mai".

A cewarsa, ya kamata tattaunawar da shugabannin biyu suka yi, ƴan ƙasa su gani a ƙasa, "gudunmawa da taimakon da Rasha za ta kawo wa ƙasar nan tamu, ta zama hanya wata ta ci gaban ƙasa, da bunƙasar tattalin arziki".

"Kada ya zama hulɗa ce ta neman ƙawance dangane da rashin jituwar da ke tsakanin Rasha da Amurka da sauran ƙasashen Yamma," in ji shi.

A nasa ɓangaren, Alassane Intanarak ya ce babu wani abin a zo a gani game da hulɗar Nijar da Rasha saboda a ganinsa "da Amurka da Faransa suna kawo wa ƙasar tallafi, Rasha ba ta yin haka."

"Kuma suna yaƙi kan abin da ya shafi haƙƙin ɗan'Adam kuma shi Vladimir Putin ba ruwansa da wannan, Rasha ba ruwanta da wani zancen dimokuraɗiyya ko mulki nagari." in ji Intanarak.

 
People are also reading