Home Back

Duk Sanda Na Dora Biro Zan Yi Rubutu, Nishadi Da Annashuwa Na Lullube Zuciyata – Maryam

leadership.ng 2024/5/19
Duk Sanda Na Dora Biro Zan Yi Rubutu, Nishadi Da Annashuwa Na Lullube Zuciyata – Maryam

MARYAM ABDUL’AZIZ wacce aka fi sani da MAI KOSAI tana daya daga cikin matasa marubutu musaman a kafofin sadarwa na zamani. Ta bayyana wa masu karatun irin gwagwarmayar da ta sha wajen ganin ta fara isar da sakonni ga al’umma ta fannin rubuce-rubuce, har ma da wasu bayanan masu yawa. Ga dai tattaunawarta tare da PRINCESS FATIMA ZARAH MAZADU Kamar haka:

Ya sunan marubuciyar?
Sunana Maryam Abdulaziz, wacce a duniyar Marubuta a ka fi sanina da Mai Kosai.

Ko za ki fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
An haife ni a garin Kano na taso a garin Kano, inda na yi karatun firamare da karamar sakandare a makarantar ‘Ikramul-Adfal’, daga nan na zana jarrabawar ‘Science and Technical’ inda na samu nasara har na tafi makarantar ‘Girls Science College (Garko), na kammala babbar sakandare a shekarar 2016 ban samu damar ci gaba da karatuna ba sai a shekarar 2019 in da na tafi makarantar ‘Aminu Kano College Of Education (Akcoe)’ na yi NCE a can. Yanzu haka ina nan ina kasuwancina kasancewar an gama karatu amma ba a samu aiki ba. Bangaren karatun islamiyya kuwa na yi makarantu da dama, daga ciki na yi ‘Madarasutul Tahfizul Kur’an’ da ke nan Mandawari kusa da ‘Sahad Store’, a nan na sauke alkur’ani mai girma, na kuma haddace wani abu daga ciki, na yi ‘As’habul khafi’, ita ma na yi sauka a nan, na yi ‘Sheik Jafar’, sai dai ban kai ga yin sauka ba wani uzuri ya yanko wa rayuwata na bar makarantar, kadan daga cikin makarantun da na yi ke nan na islamiyya. Ina da aure, sannan ina kuma tare da iyayena da kuma kannena.

Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma fannin rubutu?
Abin da ya ja hankalina na fara rubutu shi ne; Ganin yadda mutane da dama suke kaunar karanta littafi, sai na ce to ai zan iya ni ma rubuta labarina wanda daga haka zan isar da sakona cikin sauki ga al’umma, tun da na ga sun raja’a kan karatun littafi da saurara, kuma ta wannan hanyar ana iya nunawa al’umma hanyar gyara da ci gaba.

Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
To gwagwarmaya an sha ba a sha ba, sai dai zan iya cewa lokacin da na fara rubutu Alhamdu lillah, kuma a duk sanda na dora biro kan littafi na yi rubutu ina jin wani nishadi da anshuwa suna lullube zuciyata, sai dai kawai na ce Alhamdulillah amma dai an sha gwagwarmaya, musamman da ya kasance lokacin ina Jss 2 na fara rubutu, to ko gida iyayena ba su sani ba haka kuma kullum cikin taka-tsan-tsan nake ka da wani ya ankara, saboda ko littafin idan na yi rubutu cikinsa ajjiya nake bayarwa gudun kada a gani a ce za a hana ni zuwa makarantar ma gaba daya, tun da za a ce ke nan ba karatu nake yi ba sai wasa.

nishadi

Ya farkon farawar ya kasance?
To farkon fara rubutuna da dare nake yi, saboda ina ganin kar na yi rubutu a gwasale ni, a ce sam-sam bai yi ba, sannan kuma ga gida ba su sani ba, ko lokacin da nake ‘boarding’ idan na ji ‘idea’ ta fado na kan dau littafi na rubuta, don har ‘yan ajinmu suka gano ai ina rubuta littafi, tunda wani lokacin za a ari littafina to a tsakiya ko can karshe za a ci karo da labari. Haka bayan na gama makaranta ko da na dawo gida ban saki jikina ba saboda gudun kar a gano a yi min fada, wanda daga karshe kuma na jajirce na yi ta maza na cire tsoro na tunkari mamanmu da batun, Alhamdu lillah kuma ta goya min baya ta karfafa min guiwa, mahaifina kuwa da ta sanar masa bai hana ba ya ce ai abu ne mai kyau amma indai san abin da zan dinga rubutawa wanda zai kawo wa al’umma ci gaba, wanda mutane idan sun karanta za su karu ba wanda za a yi Alla-wadai da ni ba.

Kamar wane bangare kika fi maida hankali a kai wajen yin rubutu?
Na fi mayar da hankalina wajen rubuta labarin Soyayya, zamantakewa, musamman tsakanin ma’aurata da kuma yanayin rayuwa.

Za ki yi kamar shekara nawa da fara rubutu?
Na shafe a kalla shekaru goma zuwa sha daya, idan a online ne kuma shekaru takwas.

People are also reading