Home Back

Ƴan Majalisa sun fusata ganin yadda aka yi watsi da aikin haƙar ɗanyen mai a yankin Bauchi da Gombe

premiumtimesng.com 2024/7/1
Na ja kunnen kamfanonin da za su yi aikin haƙo mai a rijiyar Kolmani, su ji da mutanen waɗannan yankuna – Buhari

Mako ɗaya bayan Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta fara gagarimin aikin haƙo ɗanyen mai a Jihar Ogun, Majalisar Tarayya ta nemi jin dalilin da ya sa aka dakatar da aikin haƙar ɗanyen man fetur a yankin Kolmani da ke Jihar Gombe da Bauchi.

Cikin makon jiya ne dai Gwamnatin Tarayya ce za ta fara gagarimin aikin haƙo ɗanyen man fetur a Jihar Ogun

Gwamnatin Tarayya za ta fara gagarimin aikin haƙar ɗanyen man fetur a Jihar Ogun, kamar yadda Ƙaramin Ministan Fetur, Lokpobiri ya tabbatar.

Ya ce hakan ya zo ne daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke buƙatar ƙarin kuɗaɗen shiga a ɓangaren ɗanyen mai da gas.

Lokpobiri ya ce za a fara aikin haƙar a wasu wurare a faɗin Jihar Ogun, saboda Jihar ko tantama babu akwai ɗanyen mai a cikin ta.

Ƙaramin Ministan Fetur, Heineken Lokpobiri, ya bayyana haka a ranar Juma’a, yayin da ya kai ziyara Ofishin Gwamnan Jihar Ogun, a Abeokuta, babban birnin Jihar.

Lokpobiri ya kai ziyarar tare da manyan masu hannu a harkokin man fetur da gas daban-daban, cikin su har da Shugaban NNPCL, Mele Kyari.

Ya ce Jihar Ogun na ɗaya daga ɓangaren Dahomey Basin, wurin da ake da kyakkyawan zaton akwai ɗanyen mai kwance maƙil a ƙasa.

Ya ce sun kai ziyara Jihar Ogun ne domin su nuna irin gaggawar fara aikin wanda Gwamnatin Tarayya ke so a yi, domin ƙara samun hanyoyin kuɗaɗen shiga ta hanyar ɗanyen mai.

Ya ce ɗanyen mai ne hanya mafi saurin kawo wa Najeriya kuɗaɗen shiga masu tarin yawa.

A zamanin mulkin Buhari an ƙaddamar da aikin haƙar ɗanyen mai a yankin Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.

Sai dai kuma tun bayan ƙaddamar da aikin, har yau shiru ka ke ji babu labari kuma babu ƙarin bayani.

Majalisa Na Neman Sanin Dalilin Dakatar Da Aikin Haƙo Ɗanyen Mai A Kolmani:

A ranar Laraba ce kuma Majalisar Wakilan Najeriya ta nemi Gwamnatin Tarayya ta yi mata ƙarin bayani a kan dalilan da suka janyo dakatar da ci gaba da aikin haƙo mai a yankin Kolmani da ke Gombe da Bauchi.

A watan Nuwambar 2022 ne, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ƙaddamar da aikin fara haƙo mai a yankin Kolmani da ke iyakar jihohin Bauchi da Gombe.

Sai dai shekaru biyu, bayan fara wannan aiki, ‘yan majalisar sun ce aikin ya tsaya.

Inuwa Garba, Ɗan Majalisar Tarayya ne daga Jihar Gombe da ya gabatar da koken, ya shaida wa BBC cewa a gaban jama’a da dama tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi alƙawarin ci gaba da wannan aiki, hasali ma shi kan sa shugaban ƙasa na yanzu ya na wajen. “To amma abin mamaki shi ne kullum aikin sai samun komawa baya yake.”

Ya ce, “A yanzu kamfanonin da ke aikin haƙo man sai tattara kayans u suke yi, suna barin wajen, kamar dai ƙoƙari ake a yi watsi da wannan aiki.”

“Ni da kai na gudanar da bincike, don na je wajen na duba kuma muna magana da mutanen mu. NI fa ɗan yankin ne domin daga jihar Gombe na ke, kuma wannan man da ake tonowa a tsakanin jihar mu ta Gombe da Bauchi wajen yake.” inji shi.

Inuwa Garba, ya ce wannan tono man da aka ce za a yi duk ɗan yankin hankalin sa a tashe ya ke domin dakatar da aikin ko tafiyar hawainiyar da aikin ke yi ba ya yi musu daɗi.

Ya ce, ”Wannan dalili ne ya sa na gabatar da ƙudirin domin a ceto mu daga cikin halin da muke ciki ganin yadda ita kanta Najeriyar ke tafiya.”

Ɗan Majalisar wakilan ya ce tunanin da mutane ke yi ko matsalar tsaro ce ta sa aka dakatar da wannan aiki, ba haka ba ne, domin batun matsalar tsaro gwamnonin yankin ko jihohi biyu na Gombe da Bauchi, sun haɗa kai da sarakunan gargajiyar yankin da ma ‘yan majalisun yankin don kawar da matsalar, kuma Alhamdulillahi babu wannan matsala, don haka ba rashin tsaro ne ya sa aka dakatar da aikin tono mai a wajen ba.

“Yanzu wannan waje na nan ana ta noma da kiwo babu wata matsala, mu dai kawai mun ga kamfanonin da ke wannan aiki suna ta kwashe kayan su suna tafiya aiki ya tsaya ai dole hankalin duk wani ɗan yankin ya tashi.” Inji ɗan majalisar tarayyar.

”Mu abin da muke so yanzu a yi shi ne Shugaban Ƙasa Bola Tinibu, ya tuna da alƙawarin da ya yi a gaban mutane cewa lallai zai tabbatar da an ci gaba da wannan aiki na tono mai, don haka muna so yanzu mu ga an ci gaba da wannan aiki tare da sanya kuɗin da zai isa a yi aikin don mu ma muna so mu ga an yi wani abin a zo a gani a ɓangaren Arewa.”

People are also reading