Home Back

Bola Tinubu Ya Tsige Shugaban Hukumar PSC, Ya Naɗa Wanda Zai Maye Gurbinsa

legit.ng 2024/7/5

FCT Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya maye gurbin Solomon Arase a matsayin shugaban hukumar jin daɗin ‘yan sanda (PSC) ta kasa.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ne ya bayyana wannan sauyin da aka samu a wata sanarwa da ya fitar ranar Litini.

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Bola Ahmed Tinubu ya yi sauye-sauye a hukumar jin daɗin ƴan sanda ta ƙasa Hoto: DOlusegun Asali: Facebook

Ya ce DIG Hashimu Argungu (mai ritaya) shi ne sabon shugaban hukumar jin dadin ƴan sanda, kamat yadda Daily Truat ta ruwaito.

Shugaba Tinubu ya kuma amince da nadin Cif Onyemuche Nnamani a matsayin Sakataren PSC da DIG Taiwo Lakanu (mai ritaya) a matsayin mamban gudanarwa.

"Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin DIG Hashimu Argungu (Rtd) a matsayin shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Shugaban ƙasar ya kuma amince da nadin Cif Onyemuche Nnamani a matsayin Sakataren hukumar da DIG Taiwo Lakanu (Rtd) a matsayin mamba gudanarwa.

"Naɗin zai tabbata ne bisa sahalewar majalisar dattawa. Haka nan kuma shugaban zai nada sauran mambobin gudanarwa na PSC nan gaba kaɗan."

- Ajuri Ngelale.

Bugu da kari, Bola Tinubu ya naɗa Mista Mohammed Sheidu a matsayin babban sakataren asusun rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPTF) ba tare da bata lokaci ba.

Asali: Legit.ng

People are also reading