Home Back

An buɗe rumfunan zaɓe a Birtaniya

bbc.com 3 days ago
.

Yanzu haka dai an bude rumfunan zabe a babban zaben Birtaniya,, inda miliyoyin masu kada kuri'a ke shirin zabar yan majalisa, da kuma sabon Firaminista.

Dole ne masu zabe su gabatar da katinsu na shaida kafin kada kuri'a a rumfunan zabe.

Za a rumfe rumfunan ne da karfe 10 na dare agogon kasar da kuma na Najeriya, inda a lokacin ne kuma ake sa ran sakin sakamakon farko.

BBC ba ta da damar kawo muku rahotannin yakin neman zabe ko na siyasa da suka danganci zaben yayin da ake gudanar da shi, to amma za mu rika kawo muku bayanai daga rumfunan zaben da kuma yadda abubuwa ke gudana.

Wannan dai shi ne karon farko da al’ummar Birtaniya za su nuna wata shaida kafin su zaɓi wanda suke so.

Da dama daga cikin ƴan ƙasar sun kaɗa kuri’un su ta akwatun gidan waya.

Zaɓen zai kasance wani babban ci gaba a ƙasar.

Babu dai wata jam’iyya da ta taba cin zabe a kasar sau biyar a jere, wanda hakan shi ne tsagwaran gaskiya, da ke ci gaba da zama barazana ga Rishi Sunak.

Haka kuma babban ƙalubale ne ga shi ma ɗan takara Labour Sir Key Starma, kasancewar jam’iyyar sa shekarunta 19 rabon ta da ta ci zaɓe.

People are also reading