Home Back

Ali Nuhu Ya Bayyana Yadda Zai Tallafawa Matasa Masu Hidimar NYSC a Najeriya

legit.ng 3 days ago
  • Shahararren jarumin Kannywood, Ali Nuhu Muhammad ya gana da shugabar hukumar NYSC ta jihar Filato, Esther Ikupolalati
  • Ali Nuhu ya bayyana cewa zai tabbatar da walwalar masu yiwa ƙasa hidima da aka tura masana'antarsu ta shirya fim
  • Har ila yau, Ali Nuhu ya ce yana duba yiwuwar yadda za su inganta harkar koyon sana'a da hukumar NYSC ke koyawa matasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato - Shahararren jarumin Kannywood, Ali Nuhu Muhammad ya fara kokarin bayar da gudummawa ga matasa masu hidimar NYSC.

Ali Nuhu ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da ya yi da shugabar hukumar NYSC ta jihar Filato, Esther Ikupolalati.

Ali Nuhu
Ali Nuhu zai tallafi matasa masu NYSC. Hoto: Ali Nuhu Muhammad Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan ne cikin wani sako da Ali Nuhu Muhammad ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ali Nuhu zai tallafi yan NYSC

Jarumi Ali Nuhu ya ce zai tabbatar da cewa matasan da aka turo masana'antarsu sun samu wadatattun kayan aiki domin kwarewa.

Ya kara da cewa sun yi tanadi domin tabbatar da walwalar matasan da basu gudunmawar da ta kamata.

Za a koyawa 'yan NYSC sana'ar fim

Haka zalika Ali Nuhu ya ce sun tattauna kan yadda za a shigar da koyon wasan kwaikwayo cikin sana'o'in da NYSC ke koyawa matasa.

Ali Nuhu ya ce hakan zai buɗe kofa ga matasan wajen koyon sana'o'i daban-daban domin dogaro da kai.

Jarumin ya ce shigo da harkar koyon fim cikin NYSC zai taimaka wajen habaka tattalin arzikin Najeriya.

A karshe, Ali Nuhu ya ce yana da tabbas kan cewa haɗakar za ta haifar da ɗa mai ido wajen inganta NYSC da ba matasan gudunmawa.

Hadiza Gabon ta shawarci mata

A wani rahoton, kun ji cewa shahararriyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu gabon ta ja hankalin ƴan mata masu shirin shiga sana'ar fim.

Hadiza Gabon ta ce abin da yafi dacewa da yan mata shi ne yin aure ko komawa makaranta domin inganta rayuwarsu maimakon shiga sana'ar fim.

Asali: Legit.ng

People are also reading