Home Back

Gwamnan Kano Ya Nemi EFCC Ta Fitar Da Sakamakon Binciken Bidiyon Dala Na Ganduje

leadership.ng 2024/5/14
Gwamnan Kano Ya Nemi EFCC Ta Fitar Da Sakamakon Binciken Bidiyon Dala Na Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje na ci gaba da fuskantar matsin lamba dangane da binciken bidiyon dala da ya taba ɓulla wanda ake zargin sa da karɓar cin hanci a hannun wasu ‘yan kwangila.

Hakan ya biyo bayan wutar da magajinsa a kujerarsa ta gwamnatin Kano, Abba Kabir Yusuf ke ci gaba da hurawa kan ci gaba da binciken Ganduje, inda ya nemi hukumar EFCC ta fitar da sakamakon sahihancin bidiyon dala na Ganduje.

Sai dai, Ganduje ya mayar da martani kan zargin da gwamnatin jihar ke masa, inda ya ce wannan ba komai ba ne face ɓata lokaci da ke nuni da cewa babu wani abu da Abba Kabir Yusuf ya taɓukawa Jihar Kano a cikin watanni takwas da ya kwashe yana mulki.

Sai dai Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ce a cikin shekaru 8 da Ganduje ya kwashe yana mulkin jihar Kano ba wani abu da gwamnatinsa ta yi face karkatar da kudade da kuma cin hanci da rashawa da ya yi katutu a gwamnatin.

Gwamnan ya mayar wa Ganduje da martani dangane da sukar gwamnatinsa a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun kakakinsa Yusuf Tofa, a ranar Lahadi.

Ya ce kamata ya yi Ganduje ya mayar da hankali kan zarge-zargen cin rashawa da ke gabansa ba wai ɓata lokacinsa ba wajen saka wa gwamnatinsa ido.

Abba, dai ya nemi hukumar EFCC da ta fito da binciken bidiyon dala kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa Ganduje, wanda ya ce yana cikin yunƙurinsa na ganin ya dawo da martabar Kanawa da Ganduje ya zubar a idanun ‘yan Nijeriya.

People are also reading