Home Back

Mun shiga damuwa kan rashin cinikin Raguna a sallar bana – Mai sayar da Dabbobi a Kano

dalafmkano.com 2024/7/3

Masu sana’ar sayar da Dabbobi, na ci gaba da kokawa a jihar Kano, bisa yadda suka samu ƙarancin kasuwar Dabbobi a babbar sallar bana, biyo bayan rashin kuɗi a hannun jama’a.

A zantawar Dala FM Kano, da wani mai sana’ar sayar da Dabbobi, a kasuwar Awaki ta Gandu a jihar Kano, Mallam Sule Sheka, ya ce a shekarar da ta gabata yakan sayar da raguna guda Ɗari zuwa sama a rana, amma a wannan shekarar baya wuce guda biyar a rana.

Mallam Sule Sheka, ya kuma ƙara da cewa, Raguna a bana sun yi tashin Gwauron zabi, amma kuma duk da hakan babu masu saye, domin ba ma su fiya zuwa kasuwar ba saboda rashin kuɗi.

“Raguna a bana suna farawa ne daga Naira dubu 100, dubu 130,000, har Naira dubu Ɗari Tara, da kuma Miliyan Ɗaya, amma a hakan babu masu saya, “in ji shi”.

Malam Sule Sheka, mai Dabbobi, ya kuma ce sun shiga cikin damuwa a bana bisa rashin cinikin Dabbobi, lamarin da ya kawo musu koma baya a batun kasuwancin su a bana, inda ya nemi ɗaukin mahukunta kan sauƙaƙa farashin kayayyaki domin a samun sauƙi.

People are also reading