Home Back

"Na Yi Dana Sani": Fitattun Mawaƙan Najeriya 2 Sun Gwabza Yayin da Alaƙarsu Ke Ƙara Tsami

legit.ng 2024/5/18
  • Fitattun mawakan Najeriya, Ayodeji Balogun da David Adeleke sun sake gwabzawa yayin suke ci gaba da gasa
  • Mawaki Wizkid ya yi shagube ga Davido a shafinsa na X inda ya ke sukarsa kan wani faifan bidiyo da ya wallafa
  • Daga bisani Davido ya yi martani mai zafi inda ya ce ya yi da-na-sanin kokarin taimakonsa a baya saboda ci gabansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Alaka na ƙara tsami tsakanin fitattun mawakan kudancin Najeriya, Ayodeji Balogun da David Adeleke a kwanakin nan.

A daren jiya Litinin mawaki David Adeleke da aka fi sani da Davido ya rinjaɓe da Ayodeji Balogun da aka fi sani da Wizkid wanda ya ɗauki hankali a kafofin sadarwa.

Mawakan Najeriya, Wizkid da Davido sun caccaki juna a kafofin sadarwa
Mawaki Davido da Wizkid sun soki juna yayin da alaƙarsu ke ƙara tsami. Hoto: @wizkidayo, @davido. Asali: Twitter

Musabbabin rikicin Wizkid da Davido

Rikicin ya fara ne bayan Wizkid ya yi shagube ga fitaccen mawaki Davido a shafin X wanda aka fi sani da Twitter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mawakin ya caccaki Davido kan wani faifan bidiyonsa ya durkusa ya na addu'a da kuma kuka bayan wani mai goyon bayansa ya roke shi ya sake sabuwar waka.

Wallafar mawakin ta dauki hankalin mutane da dama a kafafon sadarwa inda suke tambayar mene damuwar mutanen biyu.

Daga bisani, Davido ya yi martani mai zafi wanda ya wallafa a shafukan sadarwa kan mawaki, Wizkid.

"Yanzu kam babu wanda ya san wadannnan shirmen wakokin naka."

- Davido

Davido ya watsawa Wizkid baƙar magana

Davido ya ce mutane da dama yanzu sun bar sauraron wakokinsa inda ya ce Wizkid ya rasa magoya bayansa.

Wizkid ya yi gaggawar mayar da martani a shafin X ga Davido inda ya ce suna bukatar addu'a.

"Kun san meye, babu komai, rikitattun mutane kuna neman addu'a, ina muku addu'a."

- Wizkid

Davido daga bisani ya sake martani da kiran Wizkid a matsayin marar lafiya inda ya ce ya yi da-na-sanin niyyar taimakonsa a baya.

Fitacciyar mawakiyar yabo ta rasu

A wani labarin, kun ji cewa wata matashiyar mawaƙiyar yabon addinin Kirista, Morenikeji Adeleke ta riga mu gidan gaskiya.

Marigayiyar ta rasu ne a ranar Asabar 27 ga watan Afrilu inda aka bayyana ta a matsayin mace mai taimakon jama'a.

Asali: Legit.ng

People are also reading