Home Back

Rikicin Sarauta: “Babu Ruɗani a Kano, Sanusi II Ne Halastaccen Sarki,” Inji NNPP

legit.ng 2024/7/6
  • Jam'iyyar NNPP ta dage kan cewa har yanzu Muhammadu Sanusi II ne halastaccen sarkin Kano duk da hukuncin kotun tarayya
  • Kakakin NNPP, Ladipo Johnson ya ce babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sauraron shari'ar saboda sarauta alfarma ce ba 'yanci ba
  • Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature ya yi kira ga jama'a da su yi watsi da batun hukuncin babbar kotun tarayyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Kakakin jam'iyyar NNPP, Ladipo Johnson, ya dage kan cewa babu rudani a game da rikicin shari'ar sarauta da ya mamaye jihar Kano.

Mista Ladipo ya ce har yanzu dai, Muhammadu Sanusi II shi ne halastaccen Kano, biyo bayan hukuncin babbar kotun tarayya a jihar.

Jam'iyyar NNPP ta yi magana kan rikicin sarautar Kano
Jam'iyyar NNPP da gwamnatin Kano sun dage cewa Sanusi II ne halastaccen sarki. Hoto: @masarautarkano Asali: Twitter

"Sanusi II ne halastaccen sarki" - Ladipo

Da yake zantawa da jaridar Newscentral, Mista Ladipo ya ce hukuncin da babbar kotun tarayyar ta yanke ba shi da tasiri saboda ba ta da hurumin sauraron shari'ar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sarauta ba wai 'yanci ba ne, alfarma ce, don haka babbar kotun tarayya ba ta da hurumin a tsoma baki a lamarin jiha, don haka, Sanusi II ne sarkin Kano, babu jayayya."

- A cewar kakakin NNPP.

Ya kara da cewa lamuran da suka shafi sarautar jihar wani hurumi ne na gwamna, kuma ko ba komai akwai umarnin babbar kotun jiha da ya haramta a tsige Sanusi II daga sarauta.

"Dalilin mayar da Sanusi II mulki" - Sanusi

Shi ma da ya ke amsa tambayoyi, mai magana da yawun Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano, Sanusi Bature ya ce an mayar da Sanusi II kan mulki ne saboda dawo da martabar masarauta.

Ya kara da cewa da ace ba ayi wannan gyaran ba, to da kowanne gwamna idan ya hau mulki zai iya sauke sarki ya naɗa wanda yake so, inji rahoton The Guardian.

Ya dage kan cewa Sanusi II ne sahihin sarkin Kano yayin da yake kira ga jama'a da su yi watsi da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yi.

An ba da umarnin fitar da Sanusi II daga fada

A wani labarin, mun ruwaito cewa babbar kotun tarayya da ke da zama a Kano ta ba da umarnin a fitar da Muhammadu Sanusi II daga fadar sarkin Kano.

Alkalin kotun, Mai shari'a S.A Amobeda ya ce ya ba da wannan umarnin ne domin tabbatar da adalci da zaman lafiya a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

People are also reading