Home Back

Haƙar Manoman shinkafa a Jigawa na dab da cimma ruwa, Ɗanmodi na dab da kawo musu ɗauki

premiumtimesng.com 2024/6/16
Haƙar Manoman shinkafa a Jigawa na dab da cimma ruwa, Ɗanmodi na dab da kawo musu ɗauki

Alhamdulillah, da dukkanin alamu kiraye kiraye da ihun da muka sha yi na shugabanni da hukumomin gwamnati a kan su duba yanayi masifa da manoman rani, musamman ma na shinkafa suka shiga a bana, ya kai ga kunnuwan su.

Kamar yadda muka sha fada a baya, a lokacin da manoman shinkafa suke tsakiyar ruwa, lokacin da amfanin ke bukatar ishasshen bayi, sai ga shi an shiga yanayin da Man Fetur yayi tashin da yafi karfin mai karamin karfin.

Wannan ta sanya dewa daga cikin manoman gudu su hakura da gonakan su, bayan sanya dunbin dukiyar su a cikin gonar.

Wasu manoman sun saida gonakan nasu a tsaye tana yabanya, a mummunan farashi, wannan yanayi ya durkusar da manoman nan.

Wannan hali da suka shiga, masifa ce, ba kawai ga manoman ba, harma da kokarin gwamnati na bunkasa kasa da abinci.

Kamar yadda Mai Taimakawa Gwamnan a kan Kafafen Yadda Labarai na Zamani yayi bayani A wata ziyara ba zata da gani da ido da Mai Girma Gwamna DANMODI ya kai ga wasu wuraren da ake noman shinkafa da suka hada Ringim, Miga, Kaugama da Kuma Auyo. Gwamnan ya ɗauki lokaci ya na tattaunawa da wasu daga cikin manoman don jin irin halin da su ke ciki, da kuma tasirin da shirin noma na kulosta ya ke fa shi da kuma yadda tallafin manoma na gwamnati ke isa kai tsaye ga manoman.

Gwamnan ya gamsu da irin wahalhalun da manoman suka shiga, har ya kara da cewa “Gaskiya ne manoma su na shan wahala a fannin tsadar taki, man fetur da sauran kayan aikin gona. A matsayinmu na gwamanti, za mu yi dukkan abin da ya dace don ganin tallafawa manoma a jihar Jigawa” Garba Mohammed.

Fatan mu a tallafawa wannan manoman don su bada gudunmawar su na bunkasa kasa da abinci.

People are also reading