Home Back

Ribadu ya yaba da aikin ginin cibiyar addinin musulunci da ake ginawa a mazaɓarsa

premiumtimesng.com 2024/6/29
Ribadu ya yaba da aikin ginin cibiyar addinin musulunci da ake ginawa a mazaɓarsa

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana jin dadinsa kan kokarin da al’umma suka yi na kafa sabuwar cibiyar addinin musulunci a mazaɓarsa ta Bako dake karamar hukumar Yola ta kudu a jihar Adamawa.

Da yake jawabi bayan ya zagaya ɓangarorin ginin da ya kunshi masallaci da cibiyar koyar da ilimin addinin Islama da sauran kayan aiki, Ribadu ya yabawa al’umma da sauran masu hannu da shuni da suka yi aikin ganin an samu nasarar aikin.

Ya yi kira da a kara himma da bada tallafin don samun damar kammala ginin da ya kai kashi 80 cikin dari da kammaluwa.

Malam Ribadu ya hori al’ummar yankin da su yi amfani da wannan katafaren ginin, idan an kammala, a matsayin wurin taron al’ummar yankin da kuma don cigaban matasan yankin.

A ƙarshe Ribaɗu ya yi alkawarin tallafawa aikin domin a kawo ƙarshensa cikin gaggawa.

People are also reading