Tura Ta Kai Bango: Mazauna Kaduna sun Fatattaki 'Yan Ta'adda, An Rage Mugun Iri a Gari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna- Wasu daga cikin mazauna jihar Kaduna sun fara daukar matakin kare kansu yayin da suka fatattaki 'yan ta'adda.
Rahotanni sun ce 'yan ta'adda sun kai hari kauyen Rugar Sojidi da Fulani ke zaune a kusa da Issan Makaranta da ke karamar hukumar Kagarko a Kaduna.
Daily Trust ta tattaro cewa sai da 'yan bindigar su ka sace mutane uku daga kauyen kafin mazauna yankin su dauki mataki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fulani mazauna Rugar Sojidi a karamar hukumar Kagarko, Kaduna sun kashe dan ta'adda daya.
Hakan ya faru ne bayan miyagun sun kai masu hari tare da sace akalla mutane uku daga kauyen kamar yadda suka saba a wasu kauyukan.
A sanarwar da kakakin rundunar 'yan sandan Kaduna, ASP Mansir Hassan ya fitar, ta tabbatar da harin.
Ya ce rundunar 'yan sanda ta kai dauki ga mazauna garin amma ta tarar sun fatattaki yan ta'addan har sun kashe daya daga cikinsu.
Kakakin ya kara da cewa an ceto dukkanin mutane ukun da aka sace, sannan an samu alburusai da bindiga kirar AK-47 da miyagun su ka gudu su ka bari.
A wani labarin kun ji cewa rundunar sojojin Nigeriya ta cafke wasu mata guda uku da ake zargi da yiwa 'yan ta'adda leken asiri a Kaduna.
An kama matan da ke fakewa da tallan zuma a bakin titin ne a kauyen Dogon Daji a karamar hukumar Kagarko a Kaduna.
Asali: Legit.ng