Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Fadi Dalilin Rashin Zaben Shugabanni Nagari a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Sani Yariman Bakura, ya yi magana kan cikar Najeriya shekara 25 a kan tsarin mulkin dimokuraɗiya.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa mulkin na dimokuraɗiyya ya fi na soja saboda damar da mutane suke da ita ta sauya shugabannin da ba su yi musu aiki mai kyau ba cikin shekara huɗu.
Ahmad Sani ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta musamman da jaridar BBC Hausa ta yi da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa duk da tasirin mulkin dimokuraɗiyya, ƴan Najeriya na yin kuskure wajen zaɓen shugabanni idan lokacin zaɓe ya zo.
Ya bayyana cewa matsalolin jahilci da talauci su ne babban dalilin da ke sanyawa ƴan Najeriya ba su zaɓen shugabanni nagari a lokacin zaɓe.
"Akwai babbar matsala da ke damun mutanen Najeriya musamman talakawa, ita ce talauci da jahilci. Domin shi talauci da jahilci yana kawo kowace irin matsala."
"Shiyasa lokacin zaɓe wasu za su zo su yi amfani da kuɗi da dukiyoyinsu sun samu an zaɓe su. Irin waɗannan abubuwan ne suka ɓata tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya."
"Amma yanzu ina ganin kowa ya ji a jikinsa, nan gaba ina ganin talakawa za su tashi tsaye a koma ga Allah a zaɓi shugabanni nagari waɗanda za su kawo canji da gyara a rayuwar al'umma.
Obasanjo ya taso Tinubu a gaba, ya bayyana manufofinsa 2 masu kuskure
- Ahmad Sani
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ahmad Sani Yariman Bakura, ya ce yin sulhu da ƴan bindiga zai matuƙar taimakawa wajen shawo kan matsalar ta'addanci da ta addabi Arewacin Najeriya.
Yarima ya bayyana cewa yin sulhu irin wanda aka yi da tsagerun Neja Delta zai taimaka wajen magance matsalar tsaro da ta baibaye jihohin Arewa.
Asali: Legit.ng