Home Back

Yahaya Bello: Shugaban EFCC Ya Yi Barazanar Yin Murabus Daga Muƙaminsa

legit.ng 2024/5/17

Shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya rantse da Alƙah cewa zai bi diddigin kes din tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello.

Mista Olukoyede ya kuma lashi takobin cewa zai yi murabus daga muƙamin shugaban EFCC na kasa idar har ba a gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kotu ba.

Ya yi wannan furuci ne yayin hira da ƴan jarida a hedkwatar hukumar EFCC ta ƙasa da ke Jabi a Abuja ranar Talata, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Ya kuma sha alwashin cewa duk waɗanda suka kawo tangarɗa a ƙoƙarin.jami'an EFCC na cafke Yahaya Bello doka za ta yi aiki a kansu.

EFCC na kokarin gurfanar da Bello ne bisa tuhume-tuhume 19 da suka hada da halasta kudaden haram, zamba, cin amana da kuma karkatar da wasu kudade har N80.2m.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading