Home Back

Ana Cikin Halin Kunci a Najeriya Jigon PDP Ya Fadi Abin da Ya Kamata a Yiwa Tinubu

legit.ng 2024/6/18
  • Jigo a jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), Cif Bode George ya buƙaci ƴan Najeriya su ƙara haƙuri da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
  • Bode George ya buƙaci a ƙarawa shugaban ƙasan shekara ɗaya domin ya cika alƙawarin da ya ɗauka na gyara ƙasar nan
  • Ya bayyana cewa shekara ɗaya da Tinubu ya kwashe a kan mulki ya yi ta ne wajen karantar gazawar gwamnatin Muhammadu Buhari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Ondo kuma jigo a jam'iyyar PDP, Cif Bode George ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙarawa shugaban ƙasa Bola Tinubu lokaci.

Bode George ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara shekara ɗaya ga Shugaba Tinubu domin ya cika alƙawuran da ya ɗauka wajen yaƙin neman zaɓe na gyara ƙasar nan.

Bode George ya shawarci 'yan Najeriya
Bode George ya bukaci 'yan Najeriya su karawa Tinubu lokaci Hoto: Chief Olabode George, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Twitter

Cif Bode George yi wannan roƙon ne a wata hira da aka yi da shi a tashar Talabijin ta Arise a ranar Juma'a, 7 ga watan Yunin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me jigon PDP ya ce a yiwa Tinubu?

Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya kwashe shekara ɗaya yana nazarin gazawar gwamnatin da ta gabace shi domin samun damar magance matsalolin yadda ya kamata.

"Shi (Tinubu) bai taɓa yin aiki a wannan matsayin ba (shugaban ƙasa). Eh za a iya cewa yana cikin jam'iyyar APC da ta kafa gwamnati (ta Muhammadu Buhari), amma akwai bambanci saboda yanzu shi ne ke jan ragamar ƙasa."
"A tunanina, ya yi amfani da shekara ɗaya ta mulkinsa domin karantar gazawar gwamnatin da ta gabace shi. Na ba shi uzurin wannan shekara ɗayan saboda yanzu ya ga yadda komai yake."
"Ina tsammanin ministocinsa za su gano waɗannan matsalolin a cikin shekara ɗaya. Ko a lokacin da Olusegun Obasanjo ya zama shugaban ƙasa a 1999, ya yi ta ƙoƙarin gano bakin zaren a shekararsa ta farko. Mu ƙarawa Tinubu lokaci."

- Cif Bode George

Tinubu ya samu yabo

A wani labarin kuma, kun ji cewa Tsohon hadimin shugaban kasa, Doyin Okupe, ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu, inda ya bayyan shi a matsayin wanda ya fi kowa cancanta a zaben 2023.

Doyin Okupe ya bayyana cewa Tinubu ya fi sauran ƴan takara irinsu Atiku Abubakar da Peter Obi cancantar jan ragamar ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

People are also reading