Home Back

Yau Za A Kece Raini Tsakanin Arsenal Da Manchester United A Old Trafford

leadership.ng 2024/6/13
Yau Za A Kece Raini Tsakanin Arsenal Da Manchester United A Old Trafford

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal zata san makomarta a kan lashe Kofin Firimiya Lig idan ta ziyarci Manchester United a filin wasa na Old Trafford da ke birnin Manchester a yau Lahadi.

Arsenal na fatan samun nasara akan abokiyar karawarta domin ci gaba da zama ta farko kan teburin gasar Firimiya, kungiyar ta Emirates Stadium ta barar da damarta na lashe kofin Firimiya a kakar da ta gabata a wasannin karshe.

Wasan wanda za a buga da misalin karfe 4:30 agogon Nijeriya, zai matukar daukar hankalin masu sha’awar kallon kwallon kafa a Duniya, duba da yadda karawa a tsakanin manyan kungiyoyin take yin zafi sosai a duk lokacin da suka hadu da juna.

Zuwa yanzu Manchester United tana matsayi na 8 a kan teburin gasar Firimiya, amma yin nasara a Old Trafford a wasan yau zai sa ta koma ta 6 wanda kuma shi ne zai kara mata kwarin guuiwar samun buga wasannin Turai a kaka mai zuwa.

People are also reading