Home Back

SHAWARAR GWAMNAN LEGAS GA ‘YAN FANSHO: ‘Kada ku yarda ku bayar da ‘yan kuɗaɗen ritayar ku sadaka a coci-coci da masallatai’

premiumtimesng.com 2024/10/6
Babajide-Sanwo-Olu
Babajide-Sanwo-Olu

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya yi gargaɗi da shawara ga ‘yan fanshon jihar cewa kada su yarda masu gina coci-coci suna karɓe wa mutane kuɗi su biyo ta kan su.

Gwamna Sanwo-Olu ya bayyana haka ranar Juma’a a Legas, yayin da yake bai wa ‘yan fansho shawarwarin yadda za su riƙa tattalin ‘yan kuɗaɗen su.

Wannan shawara da ya bayar ta tayar da hayaƙi a soshiyal midiya daga ranar Juma’a.

Yayi bayanin yayin da yake bai wa ma’aikata 2,000 satifiket na yin ritaya daga aiki, mai nuna sun shiga sahun ‘yan fansho kenan, wanda aka yi a Ikeja, ranar Alhamis.

Hukumar Kula da ‘Yan Fansho ta Jihar Legas ce ta shirya taron, wato LASPEC.

A cikin guntun bidiyon da aka riƙa watsawa a soshiyal midiya, Sanwo-Olu ya shawarce su kada su bayar da kuɗaɗen su ga masu neman gudummawar gina coci-coci ko masallatai, ko kuma ‘yan damfarar da za su matse su kusa, domin su damfare su.

Da ya ke magana da Yarabanci, Sanwo-Olu ya yi masu bayanin muhimmancin yin taka-tsantsan wajen kashe kuɗaɗe ga ɗan fansho.

“Ku yi hattara fa. Shaiɗan ya na da hanyoyi da yawa waɗanda ya ke yi wa mutum shirgar-burtu. Yanzun nan sai shaiɗan ya bijiro maka abin da kwata-kwata babu shi a tsarin da ka yi wa rayuwar ka.

“Ka maida hankali wajen yi wa kan sa wani abu, kafin ka ka karkata zuwa magance wa wani ko wasu ta su matsalar. Kuɗin nan fa kuɗin ka ne. Kai ne ka sha wahalar aiki tsawon shekaru masu yawa, ka tara abin ka. Ina farin ciki da Allah Ubangiji ya kawo ku lokacin karɓar fanshon ku.

“Kada ku karɓi kuɗi wasu kuma su kewayo su ce ku bayar da gudummawar gina masallaci ko coci.”

“Sannan kuma akwai ‘yan damfara masu ƙaryar ku bayar da kuɗi a nunka maku nunkin abin da mutum ya bayar. Duk ƙaryar banza ce. Damfara ce! 4419 ne! ‘Yan ƙaƙudubar Ponzi ne kawai. Ku yi hattara da su.” Inji Sanwo-Olu.

“Za su zo su ce maku su na neman taimakon gina coci, su na son Naira miliyan 3…”

People are also reading