Home Back

Yan adawar Togo na son 'yan kasa su musu afuwa

dw.com 2024/10/6
Shugaba Faure Gnassingbé na kasar Togo
Shugaba Faure Gnassingbé na kasar Togo

Jagororin 'yan adawa a kasar Togo sun nemi afuwar al'ummar kasar bisa abinda suka kira kasa tabuka wani abin azo a gani da suka yi na siyasa wanda hakan ya haifar musu gagarumin cikas a gwagwarmayar da suke na kwatar iko.

A birnin Lome, kakakin kawancen 'yan adawar Togo Nathaniel Olympio ya bayyana cewa sun tafka kura-kurai kana rashin jituwar da ta kunno kai a tsakaninsu ta taka muhimmiyar rawa wajen kawo musu cikas a siyasa.

Karin bayani : Karar Togo kan gyara ga kundin tsarin mulki

Duk da kalubalantarta da kawancen jam'iyyun adawa suka yi a Togo, jam'iyyar UNIR ta Faure Gnassingbé da ke kan karagar mulki shekaru 19 da suka gabata ta lashe zaben 'yan majalisar dokokin kasar da gagrumin rinjyae, lamarin da ya bata damar cimma manufofinta na sauya kundin tsarin mulki.

People are also reading