Home Back

Duniya Kenan: Watanni Bayan Mutuwar Gwamna, an Maye Gurbinsa Na Shugaban Gwamnoni

legit.ng 2024/7/7
  • Watanni kadan bayan mutuwar Rotimi Akeredolu, Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos ya karbi mukaminsa
  • Sanwo-Olu ya zama sabon shugaban kungiyar gwamnonin yankin Kudu maso Yammacin Najeriya a jiya Litinin
  • Wannan na zuwa ne bayan mutuwar Akeredolu a watan Disambar 2023 a Jamus wanda aka binne shi a watan Faburairun 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya zama sabon shugaban kungiyar gwamnonin yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Sanwo-Olu ya maye gurbin marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu a jiya Litinin 10 ga watan Yuni.

Daily Trust ta tattaro cewa Sanwo-Olu ya zama shugaban gwamnonin ne bayan zabensa da takwarorinsa a yankin suka yi.

Gwamna Sanwo-Olu ya maye gurbin Akeredolu a matsayin shugaban gwamnoni
Babajide Sanwo-Olu ya maye gurbin Akeredolu a matsayin shugaban gwamnonin yankin Yarbawa. Hoto: Babajide Sanwo-Olu. Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lagos: An zabi Sanwo-Olu shugaban kungiyar gwamnoni

Bayan Sanwo-Olu, sauran gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Lucky Aiyedatiwa daga Ondo da Dapo Abiodun na jihar Ogun.

Sairan sun hada da Seyi Makinde daga jihar Oyo da Ademola Adeleke na Osun da kuma Biodun Oyebanji na jihar Ekiti.

Wannan ganawar da kuma zaben Sanwo-Olu na zuwa ne watanni hudu bayan binne tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu.

Yaushe tsohon Gwamna Akeredolu ya rasu

Idan ba ku manta ba Legit Hausa ta ruwato muku cewa Akeredolu ya rasu a watan Disambar 2023 a kasar Jamus.

Sannan an yi bikin binne shi a watan Faburairun 2024 bayan watanni biyu kenan da mutuwarsa.

Sanar da mutuwarsa ke da wuya aka rantsar da mataimakinsa a lokacin, Lucky Aiyedatiwa domin ci gaba da rike ragamar jihar.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading