Home Back

Ma'aikatan Wutar Lantarki Sun Ji a Jikinsu Bayan Datse Wutar Barikin Sojoji

legit.ng 2 days ago
  • Ma'aikatan kamfanonin rarraba wutar lantarki a Legas sun ji a jikinsu bayan jami'an rundunar sojojin sama sun dira a ofisoshinsu
  • Jami'an sojojin sun lakaɗawa ma'aikatan duka bayan sun datse musu wutar lantarki sakamakon ƙin biyan kuɗaɗe da suka yi na wutar lantarkin
  • Shaidun ganau ba jiyau sun bayyana cewa sojojin bayan lakaɗawa ma'aikatan duka sun kuma tafi da wasu zuwa barikinsu kamar waɗanda suka yi laifi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Jami’an rundunar sojojin sama sun kai farmaki a wuraren rarraba wutar lantarki na TCN, Eko Disco da Ikeja Electric, inda suka afkawa ma’aikata tare da hana raba wutar lantarki.

Sojojin waɗanda suka zo daga barikin Sam Ethnan, da ke Bolade a Oshodi, ana zarginsu da laƙadawa ma'aikatan wuraren duka tare da tafiya da wasu daga cikinsu da ƙarfin tsiya.

Sojoji sun yiwa ma'aikatan kamfanin TCN duka a Legas
Sojojin sama sun yiwa ma'aikatan kamfanin TCN dukan tsiya a Legas Hoto: Legit.ng Asali: Original

Meyasa sojoji suka doki ma'aikatan?

Majiyoyi sun bayyana cewa sojojin sun yi hakan ne bayan an yanke musu wutar lantarki a barikin na su sakamakon ƙin biyan kuɗin wuta waɗanda sun kai biliyoyin Naira, cewar rahoton tashar Arise tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaidun ganau ba jiyau ba sun ce sojojin sun dira a ofisoshin kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN), Eko Disco waɗanda suke a Isolo da na Ikeja Electric wanda yake a titin hanyar Okota.

Sojojin sun ci galaba kan ma'aikatan da ke bakin aiki a TCN yayin da suka datse wutar da ake rabawa zuwa sauran wurare, tare da haƙiƙance cewa sai an mayar musu da ta su wutar lantarkin.

Lokacin da suka je ofishin Ikeja Electic na Oshodi da ke kan titin hanyar Okota a Isolo, sun lakaɗawa ma'aikatan wurin dukan tsiya tare da tafiya da su zuwa barikinsu kamar wasu masu laifi.

Za a ɗauke wutar lantarki a Ekiti da Ondo

A wani labarin kuma, kun ji cewa masu amfani da wutar lantarki a jihohin Ondo da Ekiti za su kasance cikin rashin wutar lantarki na tsawon watanni biyu.

Za su kasance cikin duhu ne sakamakon gyaran da hukumar kula da rarraba wuta (TCN) za ta yi a kan layin Osogbo/Akure – Ado – ​​Ekiti mai karfin 132kV.

Asali: Legit.ng

People are also reading