Lauyoyin Yahaya Bello Sun Shiga Babbar Matsala, EFCC Ta Roƙi Kotu Ta Ɗaure Su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar EFCC ta nemi babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta ɗaure wasu manyan lauyoyi biyu, Ifedayo Adedipe da Abdulwahab Muhammed kan zargin ɓata aiki.
EFCC ta shaidawa kotun cewa manyan lauyoyin sun gaza gabatar da Yahaya Bello gaban kotu wanda hukumar ke zargi da almundahanar N80.2bn.
Kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na intanet, ana tuhumar Yahaya Bello tare da ɗan uwansa Ali Bello, Dauda Suleiman da Abdulsalam Hudu kan laifuffuka 19.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan EFCC, Kemi Pinhero (SAN) ya roki kotun da ta ladabtar da Abdulwahab da Adeola saboda gaza cika alkawarin gurfanar da tsohon gwamnan.
Mista Kemi ya ce:
"Ina rokon wannan kotu mai alfarma da ta gurfanar da lauyoyin saboda sun ɓata aiki, akwai buƙatar su fuskanci hukunci, musamman tunda Adedipe yana nan, a fara ta kansa.
"Doka ta 32, sakin layi na 33 na kundin dokokin aikin mu na 2023, ya ce duk lauyan da ya gaza cika alkawarin da ya dauka a madadin kasan ko wanda yake wakilta ya saɓa doka."
Sau tari Mohammed da Adedipe sun sha daukar alkawarin za su gurfanar da tsohon gwamnan na Kogi a gaban kotu, amma sun gaza cika alkawarin.
A zaman kotun na ranar Alhamis muka ruwaito Adedipe ya shaidawa kotun cewa sun mika buƙata ga babban alkalin babbar kotun tarayya na a mayar da shari'ar zuwa jihar Kogi.
Sai dai lauyan EFCC ya dage kan cewa abin da ya tara su a kotu a ranar shi ne sanin dalilin da ya sa lauyoyin suka gaza gurfanar da Yahaya Bello duk da alkawarin da suka dauka.
A karshe dai Mai shari'a Emeka Nwite ya dage shari'ar zuwa ranar 17 ga watan Yuli idan zai duba bukatar da aka gabatar na gurfanar da lauyoyin Yahaya Bello.
A wani labarin, mun ruwaito cewa Adeola Adedipe (SAN), daya daga cikin lauyoyin da ke kare Yahaya Bello ya mika takardar janyewa daga kare tsohon gwamnan Kogi.
Mista Adedipe ya ce ba zai iya ci gaba da kare Yahaya Bello a shari'arsa da hukumar EFCC ba, abin da lauyan hukumar ya ki amince da shi inda ya ce bakin alkalami ya bushewa Adedipe.
Asali: Legit.ng