Home Back

Belgium ba za ta je Euro 2024 da Courtois ba

bbc.com 2024/5/17
Thibaut Courtois

Asalin hoton, Getty Images

Mai tsaron ragar Belgium, Thibaut Courtois ba zai buga wa kasar gasar nahiyar Turai ta Euro 2024 ba, sakamakon fama da jinya da ya yi.

Belgium ba za ta je da shi gasar da za a gudanar ba a Jamus a bana, duk da cewar yana daf da komawa yi wa Real Madrid wasanni.

Courtois, mai shekara 31, ya yi jinyar kusan gabaki dayan kakar nan, wanda ya fama raunin aka kara yi masa aiki a cikin watan Maris, wanda ya ci karo da koma baya.

Ana sa ran zai yi wa Real Madrid tamaula kafin a kare wasannin bana a cikin watan Mayu, sai dai kociyan Belgium, Domenico Tedesco ya ce ba zai je da golan gasar Euro 2024 ba.

Courtois, wanda ya tsare ragar Belgium karo 102 ya sanar a cikin watan Disamba da cewar ba zai koma kan ganiya ba da za ta sa ya taka rawar gani a Jamus a gasar da za a fara cikin Yuni zuwa Yuli ba.

Kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti ya sanar cewar yana fatan Courtois zai fara buga wa kungiyar wasa ranar Asabar a karawar da za ta yi da Cadiz a La Liga.

People are also reading