Home Back

Abinda dokar hana auren wuri a Saliyo ta ƙunsa

bbc.com 2 days ago

Asalin hoton, Khadijatu Barrie

Khadijatu Barrie
Bayanan hoto, Khadijatu Barrie ta tsere daga gida a lokacin da take da shekara 10 saboda mahaifinta ya yi yuƙurin aurar da ita
  • Marubuci, Umaru Fofana,
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Aiko rahoto daga Freetown
  • Mintuna 6 da suka wuce

Gwamnatin Saliyo ta gabatar da wata sabuwar dokar hana auren wuri, inda aka yi gagarumin biki kan hakan a babban birnin ƙasar Freetown wanda matar shugaban ƙasar Fatima Bio ta shirya.

Daga cikin baƙin da suka halarci taron akwai matar shugaban ƙasar Cape Verde da ta Namibia.

Shugaba Julius Maada ya sanyawa dokar hannu a wajen taron, daga yanzu duk wanda ya aurar da ƴar sa ƙasa da shekara 18, za a ci shi tarar dala dubu 4,000 ko kuma zaman gidan yari na aƙalla shekara 15 ko kuma duka.

Khadijatu Barrie wadda aka aurar da ƴar uwarta tana da shekara 14, ta shaidawa BBC cewa ta yi farin ciki da dokar kuma tana fatan hakan zai ceci sauran ƙannenta.

"Na so matuƙa ace tuntuni aka samar da wannan doka. da na ceci ƴar uwata da ƙawayena da sauran maƙwabtanmu, " In ji matashiyar ƴar shekara 26 wadda ke karatu a jami'a.

Mutanen Saliyo al'umma ce wadda maza ne ke yanke hukunci, saboda haka abi ne mai sauƙi mahaifi ya yi wa ƴarsa auren dole.

Ms Barrie ta fuskanci irin wannan matsala a lokacin da take da shekara 10, sai dai ta nuna tirjiya, inda ta gudu daga gida bayan da mahaifinta ya nesanta kan shi da ita.

Ta yi nasarar samun wasu malamai da suka ɗauki nauyin karatunta kuma ta samu wajen zama da tallafin asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya.

Sai dai ta ce bin umarnin dokar zai yi wahala a karkara, saboda haka akwai buƙatar a wayar da kan al'umma lungu da saƙo domin tabbatar da dokar ta yi aiki.

"Idan kowa zai fahimci abin da mata ke fuskanta, to ƙasar nan za ta samu ci gaba, " In ji Barrie.

Ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta yi ƙiyasin cewa kashi uku cikin huɗu na ƴara mata dake ƙasar ana aurar da su ƙasa da shekara 18, lamarin da ke haifar da yawan mutuwar mata wajen haihuwa, inda ƙasar ke cikin ƙasashen da aka fi samun mace-mace wajen haihuwa a duniya.

Daga cikin waɗanda za su fuskanci hukunci a cikin sabuwar dokar, akwai Ango da Iyaye ko kuma wakilan amarya da kuma wadanda suka halarci ɗaurin auren.

Matar shugaban ƙasar, Mrs Bio na kan gaba wajen yaƙi da cin zarafin mata tun bayan da mijinta ya zama shugaban ƙasar shekara shida da ta gabata, inda ta yi fatan sanyawa dokar hannu ya zama gagarumin abu.

Tun bayan da ƴan majalisar ƙasar suka amince da dokar makwannin da suka gabata, ba a samu wani bayaninta sosai a cikin ƙasar ba.

Asalin hoton, Sierra Leone presidency

Shugaban ƙasar Saliyo Julius Maada
Bayanan hoto, Ɗiyar shugaba Julius Maada Bio ta halarci wajen taron sanyawa dokar hannu

A wajen taron shugaba Bio ya ce "Ra'ayina da ƙwarin guiwata kan ƙarfafawa mata da yara guiwa abi ne da na ke yi tsawon rayuwata."

Ɗiyarsa ƴar shekara takwas na cikin waɗanda suke wajen da shugaban ya sanyawa dokar hannu.

Shugaban ƙasar mai shekara 60 ya yi bayanin yadda babansa ya rasu yana ɗan ƙarami da kuma yadda ya tashi a gaban mahaifiyarsa. Ya rasa babbar yayarsa da ya ce " Ta bani ƙwarin guiwa wajen cimma burina."

Ya kuma yaba da jajircewar matarsa wajen gwagwarmayar ƴancin mata. "Muna son mu hada hannu wajen mayar da ƙasar Saliyo inda za a riƙa ba mata dama wajen cimma burinsu. A koda yaushe na yi ammannar cewa makomar Saliyo na hannun mata."

Masu rajin kare haƙƙin al'umma sun yi maraba da matakin.

A shafinsu na X , ma'aikatar kula da harkokin ƙasashen Afirka ta Amurka, ta yi maraba da dokar, inda ta ce " Ba yara mata dokar za ba kariya ba, za ta taimaka wajen kar haƙƙin ɗan adam.

Asalin hoton, Sierra Leone presidency

Matar shugaban ƙasar Saliyo Fatima Bio
Bayanan hoto, Matar shugaban ƙasa, Fatima Bio a hannun dama tana kallon lokacin da mijinta ke riƙe da dokar da ya sanyawa hannu ta hana aurar da ƴan mata ƙasa da shekara 18.
People are also reading